Lebanon: Me ya jefa kasar cikin tashin hankali?

Wani dan zanga-zangar kin gwamnati nan-nade cikin tuta na tsaye gaban titin da aka rufe da ta ya a 14 ga watan Janairun 2020

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Lebanon na tsakiyar wani mummunan rikici da ta samu kanta na tsawon shekaru

Kasar Lebanon na cikin jimami bayan fashewar wasu sinadarai a yankin tashar jirgin ruwa da ke Beirut wanda ya kashe mutum 100 ya kuma jikkata dubban mutane.

Wannan fashewa ta zo ne cikin wani irin halin matsi da kasar take ciki, ba kawai na shawo kan annobar korona ba, har da matsalar tattalin arziki da ba a yi hasashe ba.

Wannan matsalar ta tattalin arziki ta jefa dubban mutanen kasar cikin matsanancin talauci ya kuma janyo wata gagarumar zanga-zangar kin jinin gwamnati.

Me ya faru ga tattalin arzikin kasar ne?

Tun gabanin bullar korona a kasar a farkon wannan shekarar, Lebanon ke neman fadawa matsin tattalin arziki.

Basussukan da ke kan daidaikun mutane wanda da su kasar ke samun kudaden shiga na cikin gida ne suka yi yawa, kuma shi ne na uku mafi girma a duniya: adaddin rashin aikin yi a kasar ya kai kaso 25 cikin 100 kuma kusan kaso daya cikin uku na 'yan kasar na rayuwa ne cikin talauci.

Wani mutum na kirga dalar Amurka a kasuwar musayar kudi a wani hsago a Beirut a ranar 24 ga watan Afrilun 2020

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Darajar kudin kasar ya fadi da kusan kaso 80 cikin 100 cikin watanni 10 baya.

A daidai wannan lokacin kuma mutane na cikin bacin ran gwamnati ta gaza samar da ababan more rayuwa. Kullun suna fama da daukewar wutar lantarki, ba sa samun ruwan sha mai sanyi, ba kowa ke da damar samun kulawar da ta dace ba a asibiti kuma karfin intanet din kasar na daya daga cikin marasa kyau a fadin duniya.

Da yawa na zargin manyan masu kudin kasar da dabaibaye siyasar kasar na tsawon shekaru, yayin da suka gaza samar da tsarin da zai magance matsalolin da kasar ke ciki.

Menene ke ƙara ta'azzara zanga-zangar?

A farkon watan Oktobar 2019, karancin kudaden ketare ya janyo faduwar darajar idan aka kwatanta da dalar Amurka a sabuwar kasuwar musayar kudi ta a karon farko cikin shekaru 20. Yayin da masu shigo da alkama da manfetur suka bukaci a biya su da dala, sai kungiyoyi su shiga yajin aiki.

Wata mummunar wutar daji da aka samu a kasar ya kara fito da rashin kudi da kuma kayan aikin da hukumar kashe gobara ta kasar take da shi.

Saad Hariri na magana a wani taro a Beirut a ranar 18 Oktoba 2019

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Sa'ad Hariri ya sauka daga mukamunsa a wani mataki na amsa kiran masu zanga-zangar

Ana tsaka da wannan matsalar a watan Oktoba, gwamnati ta sanya sabbin haraji kan taba sigari da fetir, haka zalika aika sako ta irin ta manhajar Whatsapp na da nasa harajin na daban.

Dubban mutane ne suka fantsama kan tituna suna bukatar Firaiminista Sa'ad Hariri ya sauka daga mukamunsa.

Guguwar zanga-zangar da aka kaddamar gaban fadar gwamnatin kasar da ke Beirut, Lebanon ranar 19 Oktoba 2019

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Zanga-zangar ta game ko ina a kasar

Wannan zanga-zanga ta shafi ko ina a kasar - kuma rabon da a fuskanci irin ta tun lokacin yakin basasar 1975-1989 - ya daidaita kasar.

Ta yaya annobar korona ta kara dagula lamarin?

Lokacin da aka fara shigowa cikin matsalar korona da mace-macen da aka samu kan wannan cuta - ya sanya gwamnati kakaba dokar kulle a watan Maris domin shawo kan cutar.

A bangare daya kuma ta tilasta wa masu zanga-zangar dakatawa amma a gefe daya kuma ta karara bayyana rikicin da ke cikin tattalin arzikin kasar.

Bakers package workers package freshly-produced bread coming off a production line at an automated bakery in Lebanon"s capital Beirut (1 July 2020)

Asalin hoton, AFP

Rashin biyan albashi ya tilasta dakatar da wasu kasuwancin, wanda hakan ya kara samar da wani wagegen gibi tsakanin darajar kudin kasar da na kasashen waje.

Yayin da farashi ke kara tashi na kayayyaki, wasu iyalan ma ba sa iya siyan abubuwan da suke bukata na yau da gobe.

Matsin tattalin arzikin ya kara haifar da wata zanga-zangar. A watan Afrilu an harbe wani matashi har lahira yayin wani rikici a Tripoli an kuma kona bankuna da dama.

A youth walks past a burnt-down branch of a Lebanese bank in al-Nour Square in Tripoli, Lebanon (12 June 2020)

Asalin hoton, AFP