Zaben Amurka: An sauya biranen da Trump da Biden za su yi muhawara saboda Covid-19

Joe Biden and Donald Trump

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Joe Biden (a hagu), ya sha gaban Donald Trump a kuri'ar ra'ayin jama'a

Muhawarar farko da ƴan takarar shugabancin Amurka Donald Trump na jam'iyyar Republican da mai ƙalubalantarsa Joe Biden na jam'iyyar Democrat za ta gudana ne a birnin Cleveland na jihar Ohio ranar 29 ga watan Satumba.

A baya an shirya yin muhawarar ce a harabar jami'ar Notre Dame da ke Indiana amma aka sauya wurin saboda fargabar yaɗuwar cutar korona.

A yanzu jami'ar Case Western Reserve da Cleveland Clinic ne za su ɗauki nauyin muhawarar.

Ƴan takarar biyu za su tafka muhawara sau uku gabanin zaɓen shugaban ƙasar da zai wakana ranar 3 ga watan Nuwamba.

Sabon wurin zai kasance cikin bangaren koyar da ilimin kiwon lafiya na jami'ar Western Reserve, kamar yadda shugaban hukumar da ke shirya muhawarar ya bayyana.

Ranar 15 ga watan Oktoba za a gudanar da muhawara ta biyu a Miami bayan da aka sauya wurin daga Jami'ar Michigan.

Muhawara ta uku kuwa za ta auku ne a birnin Nashville na jihar Tennesee ranar 22 ga watan Oktoba, inda ake sa rai mataimakin shugaban ƙasa Mike Pence zai kara da wanda ɗan takarar jam'iyyar Democrat za ta zai tsayar ranar 7 ga watan Oktoba a birnin Salt Lake.

Mista Biden ne ke kan gaba a sakamakon kuri'ar jin ra'ayin jama'a da maki 15 a fadin ƙasar, kamar yadda sakamakon da jaridar Washington Post ta gudanar tare da tashar talabijin ta ABC News ke nunawa.

Farin jinin shugaban na Amurka sai ƙara raguwa yake yi a wannan shekarar da annobar korona ke ƙara ta'adi - wanda fiye da Amurkawa 147,000 suka rasa rayukansu a dalilin ta - ga kuma zanga-zangar nuna bacin rai da dubun-dubatar Amurkawa suka yi a faɗin ƙasar bayan kisan baƙar fatan Ba'Amurken nan George Floyd a hannun ƴan sanda a watan Mayu.