Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Pantami ya taka wa hukumar NIPOST burki kan ƙara kuɗin rajista
Ministan Sadarwa a Najeriya, Dr. Isa Ali Pantami ya yi watsi da sabon tsarin kuɗin neman lasisi ko rajista a kan kamfanonin kai saƙo da Hukumar Aika Saƙonni ta Najeriya (NIPOST) ta fito da shi.
Dr. Pantami ya bayyana hakan ne ranar Asabar a wani saƙon Twitter da ya wallafa, yana mai cewa hukumar ba ta samu sahalewarsa ba domin aiwatar sabon tsarin.
"Mun samu labarin wani ƙari game da kuɗin rajista, wanda ba ya cikin dokokin da na sahale muku," in ji Pantami.
"An shaida wa shugabanku a jiya cewa su dakatar da shirin sannan su aiko da rahoto ga ma'aikatarmu zuwa ranar Litinin. Ina yi muku fatan alheri."
Daga cikin sabon tsarin da Nigerian Postal Service (NIPOST) ta fito da shi, duk kamfanin da ke zirga-zirgar isar da saƙo a faɗin Najeriya zai biya naira miliyan 10 idan zai yi rajista sannan duk shekara ya biya miliyan huɗu.
Kamfanin da ke aiki a yankuna kuma zai biya miliyan biyar ne sannan ya biya biya miliyan biyu duk shekara.
Haka ma kamfanonin da ke aiki a iya cikin jihohi za su biya miliyan biyu don yin rajista, waɗanda kuma ke zirga-zirga a cikin birane za su biya miliyan ɗaya na rajista da kuma N400,000 duk shekara.
Wannan ya haɗa da duk wani kamfani da ke aikin karɓa da isar da saƙonni a Najeriya.