NDDC: Majalisar Najeriya ta ce a mayar da kuɗin hukumar da aka kwashe

majalisa dattawan najeriya

Asalin hoton, NIGERIAN SENATE

Majalisar dattijan Najeriya ta shawarci Shugaba Muhammadu Buhari ya duba yiwuwar rusa shugabancin riƙo na Hukumar raya yankin Neja Delta kuma ya mayar da aikin kula da hukumar ƙarƙashin ofishinsa.

Buƙatar na zuwa ne daidai lokacin da majalisar ta umurci jami`an hukumar su gaggauta mayar da kuɗaɗen da suka kashe ba bisa ƙa`ida ba fiye da naira biliyan huɗu cikin asusun hukumar nan take.

Majalisar ta dauki wannan matakin ne bayan wani kwamitin da ta kafa don yin bincike kan badaƙalar kuɗi kimanin naira biliyan arba'in da ake zargi a hukumar ta NDDC ya gabatar mata da rahotonsa.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ya ruwaito cewa kuɗin da aka yi zargin hukumar ta bai wa ma'aikatan da wasu 'yan kwangila sun kai naira miliyan dubu huɗu da ɗari tara da ashirin da uku cikin wata uku a baya.

Kuɗaɗen dai sun ƙunshi kimanin N85.7m don gudanar da tafiya zuwa Burtaniya da kuma N105.5m da aka biya a matsayin tallafin karatu, sai kuma N164.2m shi ma kuɗin guzuri zuwa ƙasar Italiya.

Sauran kuɗaɗen sun hadar da N1.96 don sayen kayan kula da masu fama da zazzaɓin Lassa.

Wani ɗan majalisar dattijai, Sanata Muhammad Sani Musa ya shaida wa BBC shakkunsa game da abubuwan da aka ce an kashe kuɗaɗen a kansu.

"Ana cikin wannan takunkumi na annoba (ta korona) wai a ce an tafi London bikin saukar karatu. Jirgi na tashi ne?" Dan majalisar ya tambaya.

Ya kuma ce: "Haba! Ai abin ya yi yawa. Gaba ɗaya (kuɗaɗen) wannan tafiya da aka yi da kuɗin da suka ce an sayo magungunan Lassa fever....Ai babu Lassa, a can ƙasar tasu, ko?"

Sanata Sani Musa ya ce don haka majalisa ta umarci jami'an da abin ya shafa su mayar da kuɗaden. "Kuma (idan) aka dawo da kuɗin nan sai a sa shi a cikin asusun NDDC".

Wannan layi ne

'Buhari ya mayar da NDDC ƙarƙashin ofishinsa'

Majalisar ta kuma yi kira ga shugaban ƙasar ya rusa shugabancin riƙo na hukumar idan ya ga buƙatar yin haka, sannan a ɗauko masu binciken ƙwaƙwaf kan harkokin kuɗi don gudanar da sahihin bincike kan abubuwan da ke faruwa a hukumar.

Sanata Sani Musa ya ce sun kuma shawarci Muhammadu Buhari ya mayar da hukumar ƙarƙashin ofinsa saboda a cewarsa shi kaɗai ne jama'a za su yarda da shi a wannan hali da ake ciki.

Al'amarin na zuwa ne daidai lokacin da ita ma majalisar wakilai ke gudanar da nata bincike kan ayyukan hukumar ta raya yankin Neja Delta.

Shugaban majalisar dai ya umurci akawun majalisar a ranar Alhamis ya bi matakan da suka dace don gurfanar da ministan yankin Neja Delta a gaban kotu, bisa zargin yin karya da bata sunan 'yan majalisar.

Ministan dai Godswill Akpabio ya tura wa majalisar wakilan wasiƙa bayan da ta ba shi wa'adin kwana biyu don ya wallafa sunayen 'yan majalisar da ya yi zargin cewa suna samun fiye da kashi 60 cikin 100 na kwangilolin da hukumar raya yakin Niger-Delta ke bayarwa.

A cikin wasiƙar ministan ya yi iƙirarin cewa an jahilci kalaman da ya yi ne a gaban kwamitinta na sauraren jin bahasi game da zargin almundahana a hukumar raya yankin Neja Delta.

Femi Gbajabiamila dai ya umarci akawun majalisar ya tattara lauyoyi don bin duk matakan da suka dace wajen gurfanar da ministan a gaban shari'a kan tuhumar shirga karya, tare da shafa wa 'yan majalisa kashin-kaji.

Ya yi zargin cewa ministan da wasu jami'an gwamnati sukan yi irin wadannan karairayin ne da nufin dauke hankalin jama'a daga gaskiyar lamari, tare da shiriritar da binciken da ake yi.

Wannan layi ne