Femi Fani-Kayode: Me ya sa sarautar da aka ba shi a Zamfara ta tayar da ƙura?

Femi Fani-Kayode

Asalin hoton, Zamfara Gov

Bayanan hoto, Femi Fani-Kayode ya shahara wajen zagin Hausawa da Fulani
Lokacin karatu: Minti 3

Femi Fani-Kayode ya shahara wurin yin sharhi kan al'amuran yau da kullum a Najeriya a duk kafar da ya samu, inda a lokuta da dama ke yin kakkausar suka ga duk abin da ya shafi arewacin Najeriya da Hausawa.

Kalamansa kan ƙabilun Hausawa da Fulani sun sha tayar da jijiyoyin wuya a Najeriya musamman a shafukan sada zumunta.

Sau da dama ya fito yana zagin duk mutumin da ke da alaka da Hausawa ko kuma ya karbi wani tayi daga gare su musamman wanda ya shafi sarautar.

Hakan ne ma ya sa mutane da suka yi mamaki da ya amince aka nada shi a matsayin Sadaukin Shinkafi, a masarautar Shinkafi da ke jihar Zamfara, inda aka soma kaddamar da shari'ar Musulunci bayan komawa kan turbar dimokradiyya a 1999.

Ya sha sukar shari'ar ta Musulunci da mutanen da suka kaddamar da ita.

Tuni wasu suka fara yi masa ba'a da cewa ya zama "bawan Fulani" - ƙabilar da yake yawan suka - sakamakon karɓar sarauta daga masarautarsu.

Hotunan da aka yaɗa a shafukan sada zumunta sun nuna lokacin da aka bai wa Femi Fani-Kayode takardar shaidar naɗin na ranar Litinin.

Sarautar "Sadaukin Shinkafi" da Masarautar Shinkafi ta ba shi ta jawo ce-ce-ku-ce a ciki da wajen masarautar, inda har wasu masu muƙaman gargajiya suka ajiye muƙaman nasu.

Sarkin Shinkafi Alhaji Muhammad Makwashe ya bayyana naɗin cikin wata sanarwa da ya saka wa hannu ranar Litinin.

Femi Fani-Kayode ɗan ƙabilar Yarabawa ne daga kudu maso yammacin Najeriya kuma tsohon ministan sufurin jiragen saman kasar.

Masu adawa da naɗin nasa suna ganin muƙamin gargajiyar bai dace ba saboda zargin da suke yi wa Kayode cewa "makiyin arewacin Najeriya da jama'ar yankin arewa ne".

Dr. Sulaiman Shu'aibu Shinkafi, Sarkin Shanun Shinkafi ya ce ya ajiye sarautarsa kuma in dai ba a janye saurautar da aka ba shi ba za su kai ƙara kotu.

"Wannan sarauta da aka ba shi ta sa na ajiye sarautata ta Sarkin Shanun Shinkafi tare da wani shi ma," in ji Dr. Sulaiman.

Ya ci gaba da cewa: "Mun yi alƙawari ba za mu sake karɓar wata sarauta ba idan har ba a janye sarautar ba kuma za mu garzaya kotu domin mu tabbatar da cewa an ƙwato wannan sarauta."

Masarautar Shinkafi

Asalin hoton, Masarautar Shinkafi

Shi ma Bilyaminu Yusuf, Saradaunan Shinkafi; Alhaji Umar Bala Ajiya, Dan Majen Shinkafi; da kuma Hajiya Hadiza Abduaziz Abubakar Yari, Iyar Shinkafi sun ajiye mukamansu.

Wani malami a Jami'ar Bayero ta Kano kuma ɗan asalin masarautar ta Shinkafi, Dr. Tijjani Salihu Shinkafi ya ce sarautar "Sadauki" na nufin wanda zai iya bayar da ransa ga ci gaban masarauta kuma sam ba ta dace da Femi ba.

"Wannan abu gaskiya ya yi muni," in ji shi. "Ban ga dalili ko kwaɗayin da zai sa masarautarmu mai daraja ta ba shi (Femi) sarautar Sadauki ba.

"Sadauki na nufin mutumin da zai sadaukar da ransa da jininsa ga ci gaban masarautar da Shehu Usmanu Ɗan Fodiyo ya kafa, wadda take da alaƙa da addinin Musulunci.

"Wannan mutumin ya yi zage-zage ga kakanninmu da iyayenmu sannan ya ci mutunci Ɗan Fodiyo, ya yi ashar gare shi."

Masu sharhi na ganin irin wannan bore da wasu daga cikin masu rike da sarauta a Shinkafi suka nuna kan nadin Femi Fani-Kayode wata alama ce da ke nuna cewa ba za su ci gaba da daukar irin rainin da ya rika yi musu ba.

Karin labarai da za ku so ku karanta: