Katsina: Yadda abin fashewa ya kashe yara biyar a jihar

Asalin hoton, OTHER
'Yan sanda a jihar Katsina sun fara bincike bayan wani abu da ake zargin bam ne ya fashe a ƙauyen Yammama da ke ƙaramar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina.
Mai magana da yawun 'yan sanda reshen jihar Katsina Gambo Isah ya tabbatar wa BBC da cewa yara biyar suka mutu sai kuma wasu yaran shida suka raunata.
Da misalin ƙarfe 11:30 na safe, DPO na 'yan sanda da ke Malumfashi ya ce sun ji "ƙarar wani abu a gonar wani Alhaji Hussaini Mai Ƙwai".
Mai magana da yawun 'yan sandan ya ce, " abin da ya fashewen ya kashe yara biyar na wani mai suna Alhaji Adamu Yammama, kuma yara shida da ke zaune a ƙarƙashin wata bishiya sun ji rauni".
Gambo Isah ya shaida wa BBC cewa yaran sun je gona ne domin ɗebo ciyawa da za su bai wa dabbobi sai wannan lamari ya faru, ya ce abin da ya fashe zai iya yiwuwa gurneti ce ko kuma wani abin fashewa.
A cewarsa, "Yaran sun cika ganganci, ba su taɓa ganin abu ba sai su ce sai sun ɗauka sun ga ko mene ne".
Ya kuma bayyana cewa tuni aka tafi da waɗanda suka samu raunuka zuwa wani asibiti da ke Malumfashi domin duba lafiyarsu, kuma tuni jami'an cire bam suka isa wurin domin gudanar da bincike kan lamarin.
Jihar Katsina dai ita ce jihar da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya fito, kuma a 'yan kwanakin nan, barayi da masu garkuwa da mutane sun addabi jama'ar jihar.











