Coronavirus: Majalisar Ɗinkin Duniya ta sake ƙaddamar da asusun neman tallafi

Majalisar Ɗinkin Duniya na sake ƙaddamar da gangamin neman gudunmawar dala biliyan 10.3 don taimaka wa ƙasashe mafi talauci wajen yaƙi da annobar korona.

Jami'in ayyukan jin ƙai na Majalisar, Mark Lowcock ya yi gargaɗin cewa ana samun ƙaruwar ƙasashen da ke fama da fuskantar matsalar ƙarancin abinci saboda illar da annobar ta haddasa wa tattalin arziƙi.

Karo na uku ke nan Majalisar Ɗinkin Duniya na neman irin wannan gudunmawa tun a watan Maris, kuma kuɗaɗen da take nema a yanzu sun zarce dala biliyan goma.

Mista Lowcock ya ce ɗaukin da suke samu daga ƙasashen da suka ci gaba ya zuwa yanzu kwata-kwata bai isa ba.

Majalisar ta kuma ce mutane fiye da miliyan 265 ne ke iya fuskantar yunwa nan da ƙarshen wannan shekara.

Baya ga tallafin magance fari, za kuma a yi amfani da kuɗaɗen wajen sayen kayan aikin likitanci da gudanar da gangamin wayar da kai.

Yayin zantawa da BBC, jami'in ya bayyana dalilin da ya sa ƙasashe matalauta suka fi fama da wahala."Suna fuskantar rushewar harkokin samun kuɗaɗen shigarsu daga kayan da suke fitarwa zuwa ƙetare".

Kuma ƙalilan ne daga cikin al'ummominsu da ke zaune a wasu ƙasashe, ke iya aika kuɗi gida kamar yadda suka saba a baya, in ji shi.

Ya ce matakan kulle na hana mutane zuwa aiki da kuma samun abin biyan buƙatun rayuwa a wasu wurare kamar Yemen, inda Majalisar Ɗinkin Duniya ke ciyar da mutane sama da miliyan goma sha uku a wata, "kuɗinmu kuma sun ƙare".