Coronavirus: Masu leken asiri na Rasha 'sun yi kutse a wuraren binciken maganin coronavirus'

    • Marubuci, Chris Fox & Leo Kelion
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Technology reporters, BBC News

Hukumomin tsaro sun yi gargadin cewa masu kutse a internet na Rasha sun kai hari kan kungiyoyin dake yunkurin samar da maganin cutar korona a Birtaniya da Amurka da Kanada.

Cibiyar kula da tsaron internet ta Birtaniya NCSC tace "kusan babu makawa" masu kutsen suna aiki ne a matsayin wani "bangare na hukumar leken asirin Rasha".

Sai dai hukumar ba ta fayyace hukumomin da aka hara ba, haka kuma babu bayani ko an saci wasu bayanai.

Sai dai ta ce masu kutsen ba su kawo tsaiko kan yunkurin samar da maganin na Korona ba.

Rasha ta musanta hannu a kutsen.

"Ba mu da bayani kan ko wanene ya yi kuste a kamfanonin hada magunguna da kuma cibiyoyin bincike a Birtaniya. Za mu iya fadar magana daya - Babu hannun Rasha a duka wadannan yunkurin," a cewar Dmitry Peskov, mai magana da yawun shugaba Putin, kamar yadda kamfanin dillacin labarai na Tss ya rawaito.

Wata gamayyar hukumomin tsaro ta kasa da kasa ce ta wallafa gargadin, da suka hada da:

  • Cibiyar Kula da Tsaron Internet ta Birtaniya (NCSC)
  • Hukumar Kula da Tsaro kan Sadarwa ta Kanada (CSE)
  • Sashin Kula da tsaron Internet (CISA) dake Ma'aikatar Al'amuran Cikin Gida ta Amurka (DHS)
  • Hukumar Kula da Tsaron Cikin Gida ta Amurka (NSA)

Wata kwararriya ta ce abin lura shi ne duk da cewa gwamnatin Rasha ta musanta hannu a kutsen, ana nuna yatsa kan hukumomin leken asiri na Rashar.

"Wata shahararriyar hikima a harkar tsaron intanet ita ce, da wuya a iya gano wanda ake zargi, in ma ba abu ne da ba zai yi wu ba," kamar yadda Emily Talor ta Chattam House ta bayyana.

"A mafi yawan lokaci jami'an tsaro suna jirwaye da kamar wanka ne a maganganunsu, idan suna tunanin akwai tantama.