Buhari zai binciki yadda ake kashe arzikin kasa a Neja-Delta

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ya sha alwashin gano matsalar da ke durkusar da ci gaban yankin Neja-Delta a kudu maso kudancin kasar, duk da irin dumbin dukiyar kasa da ake sadaukarwa yankin duk shekara.

Shugaban ya bayyana hakan ne a shafinsa na tuwita a ranar Alhamis da yamma, inda ya kara da cewa ''wannan gwamnatin a shirye take wajen kawo ci gaba cikin gaggawa kuma mai dorewa a yankin."

Wannan batu na shugaban na zuwa ne a ranar da wasu jami'an tsaro suka zagaye gidan Joy Nunieh - tsohuwar shugabar Hukumar Raya Yankin Neja Delta NDDC, tare da ƙoƙarin kutsawa gidan nata don kama ta, kan wasu zarge-zarge.

Duk da cewa Shugaba Buhari bai ambaci batun Nunieh ba, amma a sakon nasa ya ce ya fayyace wa Majalisar Dokoki da hukumomin bincike da na tsaro cewa su yi kokarin yin aiki tare da juna, domin a samu damar tabbatarwa da kuma cimma gaskiya da yin ƙe-ƙe da ƙe-ƙe a harkar arzikin ƙasa.

Shugaban ya umarci dukkan hukumomi da cibiyoyin bin diddgin kudi da a yanzu suke aiki da Majalisar Dokoki su bi diddigin yadda ake kashe kudade da kuma sake fasalin hukumar NDDC da gaggawa.

''Sannan su sani cewa ina samun bayanai kan dukkan hukuncin da ake zartarwa.

''Kokarinmu na tabbatar da gaskiya ba a kan NDDC kawai ya tsaya ba, har ma ga sauran hukumomin gwamnatin tarayya. Ba z mu yi kasa a gwiwa ba," in ji Shugaba Buhari

Yadda Gwamna Wike ya ƙwaci tsohuwar shugabar NDDC daga hannun ƴan sanda

A ranar Alhamis ne gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike ya 'ceto' Joy Nunieh - daga hannun wasu ƴan sanda da suka isa gidanta domin kama ta.

Joy Nunieh ta sanar da Arise TV, wata tashar talabijin da ke birnin cewa da misalin karfe 4 na asubahin Alhamis 16 ga watan Yuli, wasu jami'an tsaro sun zagaye gidanta kuma sun yi ƙoƙarin kutsawa gidan nata.

Ta kuma ce ta hana su shiga gidan nata ne saboda sun kasa nuna mata takardar sammaci.

Daga baya ta ce ta kira gwamnan jihar Nyesom Wike wanda ya tafi gidan nata kuma ya fitar da ita bayan sun yi sa-in-sa da jami'an tsaron da suka zagaye gidan tsohuwar shugabar ta NDDC.

A wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar bayan afkuwar dambarwar, Gwamna Wike ya nemi masu hannu kan binciken da su tabbatar da babu abin da ya faru ga matar.

Amma rundunar ƴan sandan Najeriya ba ta ce uffan ba duk da buƙatar da BBC ta yi na sanin abin da ya afku.

A ranar 30 ga watan Janairun 2020 ne wata kungiyar farar hula mai yaki da cin hanci da rashawa ta rubuta korafi zuwa ga Shugaba Buhari suna cewa Joy Nunieh ta yi amfani da takardun makaranta na bogi.

Kungiyar ta yi zargin cewa ta je ta samo takardar rantsuwa daga hukumar 'yan sanda da ke cikin makarantar koyon aikin lauya game da bacewar ainihin takardunta na asali don amfani da takardar ta je kotu ta samu takardun da za ta kare kanta.

Majalisar Wakilan Najeriya ta aike wa Joy sammaci don zuwa Abuja kan wani bincike a kan cin hanci da sauran abubuwa da suka shafi hukumar NDDC.

Karin labari masu alaka