Me ke faruwa sojojin Najeriya kamar bataliya guda za su bar aiki farat ɗaya?

Majalisar wakilai ta ce tana gudanar da bincike kan harkokin sojin ƙasar da kuma kuɗaɗen da take ware musu don gano abin da ke faruwa musamman a yaƙin da Najeriya ke yi da Boko Haram.

Ta ce: " Duk kuɗaɗen da muke ba su na sayen makamai a kasafin kuɗin, ba sa isar su ne? Shin ana sayen makaman? Kuma makaman da ake saya, ba sa isar su ne?"

Shin me yake faruwa ne? (Za mu bincika) saboda mu gano maganin da za mu shawo kan wannan abu," in ji mai tsawatarwa a majalisar wakilan, Hon Muhammad Tahir Monguno.

Matakin na zuwa ne bayan wasu sojojin Najeriya 365 kimanin bataliya guda, sun sanar da muradinsu na ajiye aiki bana.

Hukumomin sojin kasar dai sun ce da ma bisa al'ada lokaci zuwa lokaci akan bai wa sojojin ƙasar da ke da sha'awar ajiye aiki damar yin murabus.

Sai dai Monguno ya ce samun sojojin da yawansu ya kai bataliya ɗaya su ce za su bar aiki a lokaci guda, ba shakka ya nuna akwai alamun rashin gamsuwa kan yadda wasu al'amura ke gudana.

"Ai kwanan nan ne ta taso.... dole akwai wani dalili da ke nuna rashin gamsuwa," in ji ɗan majalisar daga jihar Borno. "Kuma batun ya rataya a wuyanmu mu bincika".

Ya ce tuni majalisar ta tura batun ga kwamitinta mai kula da harkokin sojin ƙasa don ya bincika ya gano abin da ke faruwa.

Muhammad Tahir Monguno ya ce matuƙar ba a shawo kan wannan lamari na murabus ɗin ɗaruruwan sojojin Najeriya tashi ɗaya ba, to waɗansu ma za su ci gaba da barin aiki.

"Hakan kuma zai zama mafarin sanyaya jiki ga sauran sojojin Najeriya gaba ɗaya," cewar mai tsawatarwar.

Ya ce ba su taɓa ganin sojoji da yawa haka a Najeriya sun bayyana aniyarsu ta ajiye aiki ba, don haka a cewarsa, "sai mun bincika, mun ga ƙwaƙaf".

"Ba mu taɓa ganin sojoji 365 a lokaci ɗaya sun miƙa takardar barin aiki ba. Ba mu taɓa gani ba! Ai murabus ɗin da muke gani shi ne ba ya fin mutum uku, kuma su ma ɗin sai sun cika ƙa'idar shekarun barin aiki."

Ɗan majalisar ya nuna cewa matsalar da ke ci wa sojojin Najeriya tuwo a ƙwarya kan yadda abubuwa ke gudawa game da yaƙi da Boko Haram a arewa maso gabas, ga alama ta daɗe, tana damunsu.

Ya ce daga cikin misalan da suka sani har da wani al'amari da ya taɓa faruwa a barikin Giwa na Maiduguri, inda a shekarun bayan aka ruwaito sun harbi babban kwamandansu.

"Mun ji labari....har suka harbi babbansu, wani janaral a kan cewa ba su gamsu da yadda ake tafiyar da ayyukansu ba. Cewa ba sa samun kuɗinsu daidai kuma ba sa samu isasshen makamai," in ji shi.

Ya kuma ce sun sha ganin bidiyo na wasu sojoji da ke nuna ƙorafi, "suna cewa su ba su ji daɗi" yadda yaƙi da 'yan ta-da-ƙayar-baya yake gudana ba a nan jihar Borno.

"Har da cewa ba a kula da su sosai."

Monguno ya ce akwai ma lokacin da wani babban hafsan sojin Najeriya ya yi irin wannan ƙorafi a bidiyo. "Har ma ya kai matsayin janaral".

A cewarsa ya yi ƙorafin ne kan yadda suka ƙwaci kansu da ƙyar a wani lokaci da Boko Haram suka tunkare su.

"Ba su da isasshen makaman aiki. Ya fita ya yi magana a bidiyo, Kuma wannan babban hafsan sojan na san shi, ya zauna a Maiduguri," cewa Monguno.

Sai kuma a kwanakin nan muka ga ƙarin waɗannan sojoji wajen 365 wato ya kai bataliya ma, su ma suka ce ba su gamsu da yadda ake tafiyar da wannan yaƙin basasa ba, ɗan majalisar ya ce.