Yadda likitoci ke gudun asibitocin Port Elizabeth na Afirka Ta Kudu

A patient being carried into an emergency entrance at Dora Nginza hospital in the Eastern Cape, South Africa
    • Marubuci, Daga Andrew Harding
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin BBC na Nahiyar Afirka

A wani binciken da BBC ta shafe mako ɗaya tana yi cikin asibitocin Afirka Ta Kudu da ke cike da ƙazanta a Afirka Ta Kudu inda aka gano matsalolin da suka bayyana yadda likitoci da nas-nas ke aiki cikin babu hutu cikin mawuyacin hali saboda yawan masu cutar Covid-19 da sauran cututtuka.

Wasu ma'aikatan asibitin ma na yajin aiki, wasunsu kuma na fama da rashin lafiya bayan sun kamu da cutar korona a lardin Eastern Cape, inda lamarin ya tilastawa nas-nas su riƙa yin aikin masu shara da wankin kayan asibitin ban da rahotanni masu tayar da hankali da ke cewa jariran da ke ciki na mutuwa gabanin a haife su saboda rashin kulawa.

Wani babban likitan yankin ya bayyana halin da suke ciki a matsayin "gagarumar gazawa saboda lalacewa da rashawa ta haifar".

Wani likitan kuma ya jingina matsalar kan "rugujewar tsarin kiwon lafiya... da karyewar tattalin arzikin bangaren kiwon lafiya wanda ya durƙusar da komai sanoda rashin inganci".

President Ramphosa visits the Human Settlements, Water and Sanitation COVID-19 Command Centre at Rand Water on April 07, 2020 in Johannesburg, South Africa. Its alleged that President Cyril Ramaphosa will be briefed on the operations of the centre in response to the Covid-19 outbreak ? the Co

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugaba Cyril Ramphosa

Wadannan bayanan na fitowa ne bayan da Afirka Ta Kudu ta ɗauki matakan daƙile cutar korona tun farkon bayyanarta, amma daga baya kuma sai alƙaluman masu kamuwa da ita suka rika ƙaruwa a faɗin ƙasar, abin da ya Shugaba Cyril Ramaphosa ya gargaɗi ƴan ƙasar cewa "duhun hadari ya auka mana".

'Fargaba da matsananciyar gajiya'

Wannan matsalar ta kiwon lafiya wadda ya fi ta'azzara a birnin Port Elizabeth ya tayar da wasu muhimman tambayoyi kan yadda jami'ai masu gudanar da sashen kiwon lafiya aka bari abubuwa suka taɓarɓare cikin watannin da suka gabata.

"Akwai fargaba da gajiyar jiki da ta kwakwalwa. Muna aiki ne da ma'aikata ƙalilan tun kafin isowar cutar korona, sai ga shi yanzu mun rasa kashi 30 cikin 100 na ma'aiakatanmu," in ji Likita John Black.

Dakta Black ɗaya daga cikin kwararrun likitoci biyu ne kan cututtuka masu yaɗuwa a lardin da ke da kimanin mutum miliyan bakwai - kuma shi kaɗai ne likita a Port Elizabeth da ya amince ya gana da BBC kan matsalar. Amma akwai wasu likitoci da nas-nas kusan 12 da suka nemi mu boye sunayensu kafin suka yarda mu tattauna da su domin suna fargabar rasa ayyukansu idan aka gane sun bayyana ra'ayoyinsu.

Ɓeraye na shan jinin marasa lafiya

A asibitin Livingstone - wanda shi ne babban asibitin kulawa da masu cutar korona a gundumar - ma'aikatan kiwon lafiya na bayyana halin da aka ciki "tamkar na yaƙi ne", inda za ka taras da jini da bola a cikin ɗakunan asibitin.

Akwai kuma ƙarancin kayan kariya da ma'aikatan ke buƙata da matsanancin ƙarancin motocin ɗaukar marasa lafiya da na'urorin da ke taimakawa masu cutar korona yin mumfashi, kuma za ka ga masu jinya "suna rufa da jaridu."

A kan kuma ga ɓerayen cikin asibitin suna shan jinin marasa lafiya da sauran ruwan da ke gudana daga asibitin zuwa magudanar ruwa.

Rats in Livingstone Hospital

Asalin hoton, The Daily Maverick

Bayanan hoto, Masu shara da wanki da sauran muhimman ma'aikata na yajin aiki

"Likitoci da sauaran ma'aikatan lafiya na karbar ayyukan da suka fi muhimmanci ne kawai, inda tilas ta sa suke tsaftace ɗakunan asibitin da kayan aiki da kansu. Shugabar nas-nas ce ke wanke zannuwan gado," kamar yadda wani likita ya bayyana a sakon imel.

"A tsorace nake zuwa aiki kullum," in ji wata babbar nas.

'Mata da jariransu na mutuwa'

Likitoci masu dama sun ce ma'aikatan lafiya da dama sun girgiza saboda yadda wasu mata da jariransu suka mutu a ɗakin haihuwar asibitin Dora Nginza na Port Elizabeth saboda yawan mata masu naƙuda suka cika ɗakin haihuwa.

A flooded corridor at Dora Nginza Hospital in South Africa
Bayanan hoto, Yadda ruwa ke malala cikin wani ɗakin asibitin Dora Nginza

Wasu ma'aikatan lafiya uku ma sun tabbatar da rahotannin da ke cewa ana samun mace-macen jariran da ake daf da haihuwarsu cikin makonnin da suka gabata.

'Muna kan hanyar daƙile Covid-19'

Da aka tambaye shi kan tarin matsalolin da ke addabar ɓangaren kiwon lafiya a Eastern Cape, Dr Thobile Mbengashe ya ce "akwai wasu muhimman abubuwa da ke hana mu magance matsalolin", kuma ya ce "lallai ma'aikatan lafiya sun matsu, kuma cike suke da fargaba ...sannan aiki yayi musu yawa."

The Rev Dr Elizabeth Mamisa Chabula-Nxiweni Field Hospital was built in collaboration with the German development agency and carmaker Volkswagen (VW), the largest German investment in South Africa.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani kamfanin haɗa mota ya gina wani sabon asibiti a Port Elizabeth

Gwamnatin lardin ta nuna yadda aka gina wani katafaren asibiti a Port Elizabeth da kamfanin ƙera motoci na Volkswagen ya gina a matsayin wata alamar haɗin kai tsakanin gwamnati da bangaren ƴan kasuwa.

Sai dai likitoci a Asibitin Livingstone na ganin abu ne mai wuya a kawar da matsaloli cikin hanzari.

"Suna da gadaje 1,200, amma 200 ne kawai ke da na'urar taimaka wa marasa lafiya yin numfashi kuma ma'aikatan asibitin ba za su iya kula da marasa lafiyan da suka wuce 30 ba," in ji wani likita.

Ya kuma koka cewa ana musu ɗauke ɗai-ɗai a asibitin Livingstone da wasu asibitocin zuwa sabon asibitin na Volkwagen, tun ma kafin ya fara aiki.

Livingstone Hospital
Bayanan hoto, Matsalar tsafta ta taɓarɓare a asibtin Livingstone