Coronavirus a India: Indiyawa na yi wa Amitabh addu'ar samun sauki

Asalin hoton, ThE INDIAN EXPRESS
Masoyan Bollywood sun shirya addu'o'i na musamman ga shahararren ɗan wasan fim ɗin Indiya, Amitabh Bachchan, wanda ya kamu da cutar korona.
A makon da ya gabata, Mista Amitabh mai shekara 75 ya shaida wa miliyoyin mabiyarsa a shafin tuwita cewa an kwantar da shi a asibiti sakamakon kamuwa da wannan annoba.
Ya kuma yi kira ga waɗanda suka yi mu'amula da shi kwanaki 10 da suka gabata da su yi gwajin cutar ta korona.
Masoyan dan wasan daga kabilu daban-daban na Indiya na ci gaba da tarukan addu'o'i ga Amitabh da kuma iyalansa.
Amitabh ya shaida cewa jikinsa ba wai ya yi tsanani ba ne, sai dai ya nuna alamomin yana dauke da korona, amma hakan bai sa masoyansa yin kasa a guiwa ba, domin sun jajirce da roko don gani ya samu sauki a cikin gaggawa.
Hotunan bidiyon sun nuna yadda masoyan jarumin ke nuna bakin cikin halin da masoyinsu ke ciki.

Asalin hoton, Reuters
A tattaunawar BBC da daya daga cikin masoyin Jarumin, Satendra Tiwary, ya ce'' al'ummar Indiya da dama ba su da jarumin da ya wuce Amitabh don haka suke rokon samun saukinsa''.
Tiwary, ya ce shi masoyin Amitabh ne da iyalansa don haka ba shi da buri yanzu face ganin sun samu sauki a cikin gaggawa.
Kailash Mali, shi ma wani masoyin jarumi ne da ke cewa ''yanayin da na ji labarin Amitabh ya tsinci kansa sai nake ji kamar dan uwana na jini ne, yana cikin barazana sosai don haka nake roko ya samu sauki cikin gaggawa''.
''Ina masa fatan ya tsallake wannan jarabawar domin ba ma fatan rasa shi a yanzu.''

Asalin hoton, Reuters
Amitabh Bachchan ya yi fina-finai akalla 200 a tsawon shekaru 50 da ya shafe yana fina-finai a masana'antar Bollywood.
Mista Amitabh na daya daga cikin shahararrun jaruman fim a duniya. Yana da milyoyin mabiya a Indiya, da kudancin Asiya da sauran kasashen duniya.
Halin da Mista Amitabh da iyalansa suka tsinci kansu na nuna yadda cutar korona ke sake barazana a kasar.
Amitabh da dansa Abishek Bachchan ke kwance yanzu haka a asibiti, yayin da surukarsa Aishwarya Rai da 'yarta suka killace kansu.
Alkaluma sun nuna cewa yanzu kasar Indiya ce ta Uku a duniya inda annobar korona tafi kassarawa.











