Jada Pinkett Smith ta gaya wa mijinta Will Smith cewa ta faɗa a kogin 'soyayya' da mawaƙi Alsina

Asalin hoton, Getty Images
Fitacciyar tauraruwar fina-finan Amurka Jada Pinkett Smith ta bayyana wa mijinta Will Smith cewa ta yi soyayya da mawakin nan August Alsina.
Ta bayyana wa Smith hakan ne a wani shirinta na Facebook mai suna Red Table Talk, tana mai cewa ta tsunduma cikin "rikicin" soyayyar ne bayan sun rabu da juna.
"Lokacin da lamarin ya faru ba na tare da kai," in ji ta. "Daga wancan lokacin, bayan tafiya ta yi nisa, na fada cikin rikicin soyayya da August."
Mr Smith ya tambaye ta cewa "rikicin soyayya? Soyayya."
"Ina cike da kuncin rai kuma na karaya," a cewarta.
Taurarin biyu sun yi aure tun 1997, suna da 'ya'ya biyu, kuma yanzu sun sake aure bayan rabuwarsu.
Ma'auratan sun ce sun yi wannan tattaunawa ce domin kawar da rade radin da ake yi a kansu bayan wata hira da August Alsina ya gabatar kwanakin baya a gidan rediyo, mai taken The Breakfast Club.
A yayin hirar, mawakin ya ce yana soyayya da Pinkett Smith kuma shi kansa Smith ya "sanya albarka" ga soyayyar tasu, lamarin da ya kai ga hasashen cewa taurarin na Hollywood sun sake rabuwa.
"Babu wani mutum da zai fadi wannan magana idan ba ni ba," a cewar Pinkett Smith.
"Na fahimci abin da yake nufi da 'sanya albarka' saboda a lokacin ba ma tare domin mun rabu ba tare da wata matsala ba kuma ina ganin shi da mutum ne da ke son raba aure ba."
Ta ce ta kwashe shekaru da dama ba ta yi magana da mawakin ba.










