Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Najeriya ta ce ta dakatar da fitar da wani 'fim ɗin 'yan maɗigo'
Hukumar tace fina-finai ta Najeriya, ta ce tana neman waɗanda suka shirya wani fim da take zargin yana tallata harkokin 'yan madigo a ƙasar.
Wani jami'in hukumar shiyyar arewa maso yamma, Umar Garba Fagge, ya faɗa wa BBC cewa yanzu haka sun baza jami'ai don neman waɗanda suka shirya fim IFE, da kuma taurarin da suka fito a cikinsa.
"Waɗansu mutane ne da suka jima suna neman 'yancin masu auren jinsi, su ne ke bijiro da irin wadannan fina-finai domin jan ra'ayin yan Najeriya," in ji jami'in.
Sai dai masu shirya fim ɗin sun musanta zargin cewa IFE na yayata ayyuka da harkokin 'yan maɗigo a Najeriya.
Shi dai Umar Fagge ya ce shugaban hukumar na kasa Alhaji Adedayo Thomas, ya tara su, kuma ya ba su umarnin kamo mutanen a duk inda suke, don haka tuni suka baza jami'an tsaro ana neman su.
A cewarsa, sun dakatar da fim ɗin har sai an kai wa hukumarsu ta tantance abin da ya ƙunsa kafin ta ba da iznin fitar da shi ta kowacce irin kafa a ƙasar.
Furodusar da ta shirya Fim ɗin Pamela Adie, ta wallafa a shafinta na twitter cewa, sun shirya wani gagarumin fim na soyayya mai suna Ife, da ta kira ""Abu namu, maganin a kwaɓe mu''.
A ka'ida dole ne kowanne fim da za a fitar a Najeriya sai ya je gaban hukumar domin tantancewa, sai dai a wannan karon ta ce har zuwa yanzu bai je gabanta ba.
An yi ta ce-ce-ku-ce akan fim din a kafafen sada zumunta a kasar tun kafin a kaiga sakin sa.
A shekarar 2011 ne majalisar dattijan Najeriya ta zartar da dokar da ta tanadi hukuncin daurin da zai iya kaiwa shekaru goma ga masu neman jinsi guda.
Da ma Luwadi ko Madigo haramun ne a karkashin dokokin Najeriya, kuma kungiyoyin Musulmi da Kiristocin kasar sun hada kai wajen yin Allah wadai da dabi'ar kuma suka bada gagarumin goyon baya wajen haramta ta.
A baya, kungiyoyin masu rajin kare hakkin bil'adama a duniya sun yi ta kiraye-kiraye ga Najeriya ta halatta neman jinsi guda, kafin kasar ta yi watsi da bukatar.