Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da ya sa Amurka za ta daina bai wa ɗaliban ƙasashen waje biza
Ba za a rika kyale daliban kasashen waje su rika zama a Amurka ba da zarar an koma ba da karatu ta intanet baki daya, sai dai idan za su halarci wasu darussan da ake bukatar ganinsu a zahiri.
Ma'ikatar da ke lura da shige da fice da ta hana fasakauri sun ce za a rika mayar da mutane kasashen da suka fito matukar ba su cika ka'idojin zama a Amurka ba.
Da yawa daga cikin jami'o'in kasar sun mayar da bayar da darussa ta kafar intanet saboda annobar korona.
Babu wanda ya san adadin daliban da wannan lamari zai shafa.
Dalibai daga kasashen waje da dama ne ke tafiya Amurka don neman ilimi ko wacce shekara, nuna matukar samar da kudaden shiga ga jami'o'i saboda da yawa daga cikinsu na biyan cikakkun kudade.
Jami'ar Harvard ta sanar da cewa duka darussan da ake yi za a koma yin su ta intanet daga farkon shekarar karatu mai zuwa, har ga daliban da suke zaune a jami'a.
Amma wata sanarwa da aka fitar ranar Litinin ta ce daliban kasashen waje da ke zaune a Amurka suke karatu ta intanet suka fadi jarrabawa daga baya suka koma shiga karatu a aji ido na ganin ido ka iya fuskantar hukunci daga hukumar lura da shige da fice ta kasar na korar su daga Amurka,
Wannan doka za ta yi aiki ne ga wadanda ke neman bizar karatu da kuma dalbai masu zuwa koyan sana'o'i. Ma'aikatar tsaron Amurka ta ba da biza ga wadannan mutane har 388,839 a 2019, kamar yadda bayanan hukumar suka zayyana.
A cewar ma'aikatar kasuwanci ta Amurka daliban kasashen waje sun samar da kudin shiga da suka kai dala biliyan 45 a 2018.