Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Boko Haram: Ana ci gaba da alhinin sace mata da yara kimanin 40
Al'umma a jamhuriyar Nijar na alhinin cika shekara uku, bayan da kungiyar Boko Haram ta sace wasu mata da kananan yara kimanin 40.
Lamarin ya faru ne yayin da mayakan kungiyar suka far wa jama'a a wani kauye da ake kira Ngaleewa a yankin jihar Diffa cikin 2017.
Wasu rahotanni sun ce maharan sai da suka yi wa akalla mutanen kauyen 9 yankan rago, kafin daga bisani su tsere da wasu.
Yayin da ake cika shekara uku da sace su, har yanzu babu su babu labarinsu, ko da yake hukumomi a ƙsar na cewa suna ci gaba da bincike domin gano su, da kuma kubutar da su.
Labarai masu alaka
Karin Bayani
Sakamakon zagayowar wannan rana da aka sace mutanen, kungiyoyin kare hakin dan adam da dimokaradiya a jumhuriyar ta Nijar sun gudanar da wani taron yin bayani da wayar da kan al,umma.
Daya daga cikin wadanda suka shirya taron kuma dan asalin garin da aka kai harin, Moussa Tchigari daga kungiyar farar hula ta Alternative, ya shaida wa BBC cewa daga bisani mutum biyu sun kubuta.
Sai dai har kawo yanzu sauran suna tare da wadanda suka yi awon gaba da su, sannan kuma ana ci gaba da satar al'ummar garin.
''Har yanzu ana ci gaba da satar mutane, ya kamata gwamnati ta dauki matakai don kada abin ya zama ruwan dare, wato su riƙa shiga duk inda suke so suna daukar mutane.
Kuma kamata ya yi a nemi hanyar da za a bi don kubutar da wadannan mata da yara'' In ji shi.
Rikicin Boko Haram wanda aka fara a jihar Borno arewa maso gabashin Najeriya ya fantsama zuwa makwabtan kasashe kamar su Nijar, Chadi da kuma Kamaru.
Tun a 2015 ne Boko Haram ta rika kai wa garuruwan da ke kusa da Tafkin Chadi hari, wanda ke arewa da jihar Diffa.
Bayan da tasirin kungiyar ya fara kai wa ga kasashen da ke makwabtaka da Najeriya, sai dukkaninsu suka bijiro da shirin samar da rundunar soji ta hadin gwiwa domin yi wa matsalar taron dangi.
A yankin Diffa da ya fi fama da rikicin Boko Haram a shekarar 2015 an rufe makarantu 150 a yankin saboda hare-haren 'yan kungiyar.
Kazalika kungiyar ta kashe sojojin Nijar da dama a hare-haren da ta sha kai wa musamman cikin 'yan watannin nan, baya ga lalata makarantun Boko da ke koyar da ilimin zamani.