Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Boko Haram ta kashe sojojin Nijar a Diffa'
Mayakan Boko Haram sun afka wa wani sansanin sojoji da ke kudu maso gabashin Jamhuriyar Nijar, inda suka raunata sojoji da dama.
Wannan ne hari na farko da aka samu cikin makwanni a aksar.
Kafofin yada labaran kasar sun bayar da rahoton cewa mayakan sun isa sansanin da ke kauyen Chtima Wengu a jihar Diffa dauke da makamai.
"An samu raunuka a cikin sojojinmu wadanda aka kai su asibitin Diffa domin samun kulawar gaggawa," wani dan jarida ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.
Wata majiyar tsaro kuma ta shaida wa AFP din cewa "harin ya faru amma ba mu da adadin wadanda abin ya shafa".
Chetima Wangou karamin gari ne mai nisan kilomita 25 daga garin Diffa.
Tun a 2015 ne Boko Haram ta rika kai wa garuruwan da ke kusa da Tafkin Chadi hari, wanda ke arewa da garin Diffa.