Hagia Sophia: Shin me ya kamata ginin ya zama tsakanin Masallaci da wurin tarihi?

Lokacin karatu: Minti 4

Majalisar zartarwa ta Turkiyya za ta yanke hukunci kan ko za a mayar da wurin tarihin nan na Hagia Sophia masallaci.

An gina wurin ne a ƙarni na shida, inda sarkin tsohuwar daular ƙasar Roma na wancan lokaci Justinian ya bayar da umarnin gina wurin.

Ginin ya kasance coci mafi girma na shekaru kusan 1,000.

Hagia Sophia wanda wuri ne da hukumar kyautata ilimi da kimiya da al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya ta keɓe a matsayin wurin tarihi an taɓa mayar da shi masallaci a lokacin da Daular Othoman ta ci garin da yaƙi a 1453, sai dai an mayar da masallacin wurin tarihi a shekarun 1930.

Akwai yiwuwar a mayar da wurin tarihin masallaci idan majalisar ta zartar da hukuncinta a ranar Alhamis.

Shugaban Turkiyya Recep Tayyib Erdogan ne ya yi kira da a sauya wurin yayin yaƙin neman zaɓe a bara.

Musulmai a ƙasar sun jima suna kira da a mayar da wurin masallaci, sai dai wasu masu adawa da wannan yunƙurin sun ta sukar yin hakan.

Wannan ƙudirin ya jawo caccaka daga malaman addini da na siyasa a faɗin duniya.

Shugaban cocin Orthodox ya soki wannan yunkuri shi ma. Haka zalika ministar al'adu taƙsar Girka Lina Mendoni ta soki wannan yunkuri inda ta ce neman dawo da ɓangarancin addini ne a ƙsar ta Turkiyya.

Ta ce ba zai taɓa yiwuwa a sauya wani abu ba da hukumar kyautata ilimi da kimiya da al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya ta keɓe har sai da amincewar kwamitin harkokin gwamnatoci na hukumar.

Mataimakin darakta na hukumar ta Unesco a wata tattaunawa da wata jarida ta ƙsar Girka ya ce sai an samu amincewa hakan zai iya yiwuwa.

Ya bayyana cewa hukumar ta Unesco ta rubuta wa Turkiyya wasiƙa kan wannan ƙudiri nata, amma har yanzu babu wata amsa da ta mayar.

Mene ne tarihin wurin?

Tsohon ginin wanda wuri tarihi ne na cikin garin Santambul babban birnin Turkiyya.

Sarki Justinian na tsohuwar Daular Roma ne ya bayar da umarnin gina wurin a shekarar 532 a lokacin da ake kiran birnin Constantinople - wanda nan ne babban birnin Daular Gabashin Roma.

Injiniyoyi na ƙasar a lokacin sun kawo kayan ginin wurin ne daga ƙetaren Mediterranean domin ginin cocin.

Hagia Sophia ya zama wani wuri na musamman ko kuma tamkar gida ga mabiya addinin kirista da ke bin ɗariƙar Orthodox na kusan shekaru 900.

Sai dai a 1453, Daular Othoman ƙarƙshin mulkin Sultan Mehmed II ya ci Constantinople da yaƙi inda ya mayar da sunan garin Istanbul, wanda a hausace ake kira da Santambul, hakan ya kawo ƙarshen Daular Gabas ta Roma.

Da shigarsa Hagia Sophia, Mehmed II ya kafe kan cewa sai an mayar da cocin masallaci.

Ya halarci Sallar Juma'a ta farko a ginin cocin wanda aka mayar masallaci mako guda bayan ya ci garin da yaƙi.

Ba da jimawa ba aka gina hasumiyoyi a cikin ginin tare da cire duk wani zane ko hoto da ke da alaƙ da ɗarikar Orthodox.

Kafin kammala babban masallacin Santambul a 1616, Hagia Sophia shi ne babban masallaci a birnin.

Bayan yaƙin duniya na ɗaya a 1918, an ci Daular Othoman da yaƙi inda aka waɗanda suka ci ta da yaƙi suka karkasata.

Masu fafutukar neman 'yanci daga baya suka tashi tsaye suka kafa kasa daga ɓurɓushin Daular Othoman wadda a yau ita ce Turkiyya.

Shugaban ƙasar Turkiyya na wancan lokaci Mustafa Kemal Ataturk ya bayar da umarnin mayar da Hagia Sophia wurin tarihi.

Tun bayan sake buɗe wurin a 1935, wurin ya kasance wurin da masu yawon buɗe ido suka fi ziyarta a ƙasar.

Me yasa Hagia Sophia ke da amfani?

Sakamakon tarihin wurin na sama da shekara 1,500, Hagia Sophia na da amfani a ɓangaren addini da siaysa da kuma wasu ƙungiyoyi da ke ciki da wajen Turkiyya.

Ƙungiyoyin addinin musulunci da wasu muslmai na ta kiraye-kiraye kan batun sake mayar da wurin masallaci, inda kuma an ta gudanar da zanga-zanga kan hakan.

A 1934, an kafa doka da ta haramta gudanar da duk wani abu da ya shafi addini a wurin.

Shugaban ƙasar Erdogan ya yi irin waɗannan kiraye-kiraye a wani jawabi da ya yi lokacin yaƙin neman zaɓe a bara inda ya ce "babban kuskure ne" ,mayar da Hagia Sophia wurin tarihi, kuma tun a lokacin ya nemi masu taimaka masa da su duba yiwuwar yadda za a sake mayar da wurin masallaci.