Janar Salou Djibo na neman kujerar shugaban Nijar

Tsohon shugaban mulkin soji a jamhuriyar Nijar, Janar Salou Djibbo ya sanar da aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin kasar a babban zabe da za a yi a watan Disambae 2020.

Janar Salou Djibbo ne dai ya hambarar da mulkin Shugaba Tandja Mamadou a shekarar 2010, inda ya mika mulki ga Mahamadou Issoufou a 2011.

A ranar Lahadi ne dai Janar Djibbo ya shaida wa magoya bayan jam'iyyar PJP (Dabara) yayin wani gangamin 'yan siyasa, ya ce zai tsaya takarar neman shugaban kasar jamhuriyar domin sama wa kasar mafita a siyasance.

To sai dai tuni wasu masu takarar neman shugaban kasar a wasu jam'iyyun irin su Ibrahim Yakuba na NPN (Kishin kasa) a madadin gamayyar jam'iyyu masu hamayya, ya yi kira ga a hadu wajen kare mulkin demokradiyya.

Wannan ne dai karo na farko da Janar Salou Djibbo ya fito bainar jama'a tun bayan mika mulki ga farar hula a 2011.