Coronavirus a Kenya: 'Yan sandan ƙasar sun kashe mutane a kan takunkumin rufe fuska

Asalin hoton, Getty Images
'Yan sandan Kenya sun kashe mutum uku lokacin da wasu masu tuƙin tasi suka yi zanga-zanga kan kama abokin aikinsu saboda bai sanya takunkumin kare fuska ba.
'Yan sanda sun yi harbi a tsakiyar masu zanga-zangar a birnin Lessos da ke yammacin kasar bayan sun yi taho-mu-gama, a cewar wata sanarwa da rundunar 'yan sandan ta fitar.
Rundunar ta umarci a kama 'yan sandan da suka kashe mutane.
'Yan sandan Kenya suna shan caccaka bisa zargin yin amfani da karfin da ya wuce kima wajen tursasa wa mutane bin dokar kulle.
Yaya lamarin ya faru?
Jaridar Standard ta rawaito cewa wani baduku, wato mai gyaran takalmi, ya yi kokarin sanya baki lokacin da 'yan sandan suke dukan wani ɗan tasi saboda bai sanya makarin fuska ba.
Ita ma jaridar Daily Nation ta kara da cewa 'yan sandan suna cacar baki da ɗan tasin ne kan cin hancin shillings 50 na kasar Kenya.
Daga nan ne daya daga cikinsu ya harbe badukun, mai suna Lazarus Tirop.
Nan da nan mutane suka soma zanga-zanga kan kisansa.
Daruruwan mutane sun bi 'yan sandan ofishinsu sannan suka cinna wuta a gidan daya daga cikin 'yan sandan, a cewar Daily Nation.
Sanarwar 'yan sandan ta ce an harbe karin mutum biyu.
Ta kara da cewa rundunar 'yan sanda tana kokarin "dauka kwararan matakai a kan dukkan dan sandan da aka samu da laifi".
A watan Maris aka sanya dokar hana fita, da a wasu karin matakai na dakile yaduwar Covid-19.
An kashe a kala mutum bakwai a yankuna daban-daban a Kenya a kwana biyar na farko bayan sanya dokar, a cewar kungiyar Amnesty International.
Ranar Talata, an gurfanar da wani dan sanda a gaban kuliya bisa zargin kisan wani yaro dan shekara 13 mai suna Yasin Moyo, wanda yake tsaye a saman ginin gidansu yana kallon 'yan sanda lokacin da suke tursasa wa mutane bin dokar hana fitar.











