Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Buhari ya ce Giadom ne shugaban riko na jam'iyyar APC
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce Victor Giadom ne shugaban riko na jam'iyyar APC na kasar.
Mai taimaka wa shugaban kan harkokin yada labarai Garba Shehu ne ya sanar da hakan a shafinsa na Twitter ranar Laraba da yamma.
Ya ce shugaban ya dauki wannan mataki ne sakamakon shawarwarin masana shari'a kan halin da jam'iyyar take ciki.
Sanarwar ta ce Shugaba Buhari zai halarci taron da Victor Giadom ya kira ranar Alhamis, wanda za a gudanar ta bidiyo, tare da sa ran cewa gwamnonin jam'iyyar da shugabannin majalisar dokoki na APC za su halarci taron.
Sanarwar ta fadar shugaban kasa ta yi kira ga kafofin watsa labarai su guji yada cewa APC na cikin rikici, sannan su kiyayi ba da dama ga mutane suna fadar son ransu kan lamarin shugabancin jam'iyyar.
A makon jiya ne jam'iyyar APC ta bayyana Sanata Abiola Ajimobi a matsayin wanda zai maye gurbin Adams Oshiomhole, a matsayin shugabanta na riƙo bayan wata kotu ta dakatar da Mr Oshiomhole.
Sakataren yaɗa labaran APC na ƙasa, Lanre Issa-Onilu a cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce bayan tuntuɓar sashen harkokin shari'ah na jam'iyyar kuma bisa tanadin sashe na 14 ƙaramin sashe na 2, uku cikin baka na tsarin mulkin APC mataimakin shugabanta na ƙasa shiyyar kudu ne zai ci gaba da jagorantar APC a matsayin riƙo.
Sai dai Victor Giadom ya yi ikirarin shi ne shugaban riko na jam'iyyar bayan ya samu amincear wata kotu.
Jam'iyyar ta APC ta kara rikicewa ne bayan ta hana gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki sake tsayawa takara a cikinta sakamakon rikicin cikin gida tsakaninsa da Adams Oshiomhole.
Karin labarai da za ku so ku karanta: