Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Cocin Ingila na neman afuwa kan hannu a cinikin bayi
Bankin Ingila da Cocin Ingila sun nemi afuwa dangane da alakarsu da cinikin bayi.
A wata sanarwa, bankin da cocin cikin nuna nadama sun ce ba su da alaka ta kai tsaye da batun cinikin bayin amma sun ce suna sane da cewa tsoffin shugabanninsu sun kasance a cikin harkar dumu-dumu kuma saboda haka suna nema musu aikin gafara.
Bankin ya ce ya daina baje kolin hotunan shugabannin da suka da hannu a cinkin bayin kuma zai inganta tsarin daidaito a tsakanin ma'aikata.
Har wa yau, ita ma cocin ta Ingila ta ce duk da cewa da dama daga cikin malamansu na da hannu wajen rushe cinikin bayi amma abin kunya ne samun wasu a cocin da suka amfana daga cinikin na bayi.
Dama dai majalisar Cocin ta Ingila ta taba neman afuwa a 2006.
A ranar Juma'ar da ta gabata ne kuma wasu manyan wuraren kasuwanci a Burtaniya suka nemi irin wannan afuwa.
Neman afuwar dai ba ya rasa nasaba da irin yadda zanga-zangar neman 'yanci ga bakar fata ke kara bazuwa a duniya tun bayan da wani dan sanda farar fata a Amurka ya kashe George Floyd.
Kafin shekarar 1807 dai kasashen Turai sun mayar da nahiyar Afirka da yankin Caribbean tamkar wani fagen kama dabbobi, inda suke shiga yankunan domin kama bakar fata zuwa kasashensu domin yi musu aikin bauta.