Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Koriya Ta Arewa ta tarwatsa ofishin tuntuba tsakaninta da ta Kudu
Koriya Ta Arewa ta tarwatsa wani ofishin hadaka tsakaninta da Koriya Ta Kudu, a garin Kaesong da ke kusa da iyakar kasashen biyu.
Matakin ya zo ne 'yan sa'o'i bayan Koriya Ta Arewa ta yi sabuwar barazanar daukar matakin soji a kan iyakar kasashen.
A shekarar 2018 aka bude ofishin domin taimakawa kasashen - da ba sa ga maciji - wajen tuntubar juna. Ofishin ya kasance babu kowa a ciki tun daga watan Janairu saboda annobar cutar korona.
A cikin wata sanarwa, Koriya Ta Arewa ta ce za ta mayar da mummunan martani idan har Koriya Ta Arewa ta ci gaba da nuna halin rashin son zaman lafiya.
Ta ce "tarwatsa ofishin ya sa an cire rai daga dukkan wani fata na masu kaunar ci gaban kasashen da kyakkyawar dangantaka da zaman lafiya a yankin na Koriya."
"Gwamnati ta nuna karara cewa Koriya Ta Arewa ce za ta dauki alhakin duk wani abinda ka iya biyo baya."
Tuni Rasha ta nuna damuwa kan sabon yanayin dar-dar din da aka shiga tsakanin Koriya ta Arewa da ta Kudu.
"Muna kira da a kowa ya kai zuciya nesa," a cewar Dmitry Peskov, mai magana da yawun Shugaba Vladimir Putin.
Kamfanin dilllacin labarai na Reuters ya ce ambato wani babban jami'in gwamnatin Amurka na cewa gwamnati Trump na wasu shirye-shirye da Kawayenmu Jamhuriyar Koriya (ta Kudu)."
Zaman tankiya tsakani kasashen Koriya Ta Kudu da ta Arewa ya ringa fadada cikin 'yan kwanakin nan, wanda kungiyoyin da suka gudu daga Koriya Ta Arewa zuwa ta Kudu da suke tura sakwannin farfaganda suka ringa izawa.
Kanwar Shugaban Koriya Ta Arewa Kima Yo-Jong - wacce ake yi wa kallon wata mai karfin fada a ji - ta yi barazabar rusa ofishin a karshen makon jiya.
Dan uwanta, Kima Jong-un, shi ne yake mulkin kasar tun shekarar 2011.
An yi fatan cewa dangantaka tsakanin Koriya Ta Arewa da ta Kudu da kuma babbar kawarta Amurka za ta inganta bayan ganawar da aka yi tsakanin Donald Trump da shugaban Koriya Ta Arewa Kim a kan iyakar kasashen na Koriya, sai dai babu wani abin a-zo a-gani da ya biyo baya, kuma tun lokacin lamura sun ci gaba da tabarbarewa.
A 'yan makwannin nan Koriya Ta Arewa ta ringa yin Allah-wadai da Koriya Ta Kudu saboda kyale masu farfaganda suna tura sakonni ta kan iyakarta.
Kungiyoyin mutanen da suka sauya gudu sun ringa tura irin wadannan sakonnin ta amfani da balan-balan, ko ma ta amfani da jirage marasa matuki.
A ranar Talatar da ta gabata, Koriya ta Arewa ta sanar da cewa za ta kaste duk wata hanyar tattanaunawa da Koriya ta Kudu, kuma a karshen makon jiya Kim Yo-jong ta yi barazanar tura sojoji zuwa yankin da aka janye sojoji tsakanin iyakar kasashen.
Koriya ta Arewa da ta Kudu har yanzu suna cikin halin yaki ne, saboda har yanzu ba a cimma yarjejejniyar zaman lafiya ba bayan an gama yakin Koriya a 1953.
Menene ofishin tuntuba?
Garin Kaesong dake kan iyaka ya shafe shekaru a matsayin wata alama ta tsamin dangantaka tsakanin Koriya ta Kudu da ta Arewa.
A 2013, garin ya farfado a matsayin yankin masana'antu, wanda aka kafa stakanin Koriya ta Kudu da ta Arewa.
A lokacin da yake kan ganiyarsa, an samar da masana'antu fiye da 120, aka dauki 'yan koriya fiye da 50,000 da kuma daruruwan manajoji daga Koriya ta Kudu.
Sai dai a 2016, an rufe garin bayan hankula sun tashi, abinda ya kawo karshen alamun hadin kai.
A 2018, alamu sun nuna cewa garin zai farfado yayin da kasashen Koriya suka amince da kafa ofishin tubtuba tsakanin Koriya a Kaesong.
Bude ofishin ya bada dama ga jami'an kasashen biyu su ringa tattaunawa a kai a kai a karon farko tun bayan yakin Koriya, kuma an tsara za a dauki ma'aikata 20 daga kowace kasa.
Sai dai a watan Maris, Koriya ta Arewa ta sanar da cewa za ta janye daga ofishin - sakamakon rushewar wani taro da Koriya ta Kudu da Amurka.
Wace ce Kim Yo-jong?
A 'yan shekarun nan kanwar Shugaba Kim Jong-un ta zama mai karfin fada a ji.
Daga 2014, babban aikin Kima Yo-jong shi ne kare darajar dan uwanta, inda ta ringa gudanar da aiki a sashin n farfaganda na jam'iyyar kwaminisanci.
Lokacin da aka daga darajarta zuwa mamba a kwamitin tsara manufofi na jam'iyyar kwaminisanci, alamu sun nuna cewa ta samu karin matsayi, sai dai har lokacin babban aikinta shi ne farfaganda.
A 2018, ta dauki hankalin duniya lokacin da ta ja gasar Olympics ta lokacin bazara, ta zama ta farko a iyalan Kim da ta kai ziyara Koriya Ta Kudu.
Tauraruwarta ta ci gaba da haskawa lokacin da wanta ya nuna matukar amincewa da ita, kuma lokacin da aka daina ganin shugaban Koriya Ta Arewa a bainar jama'a saboda rade-radin rashin lafiya, an ringa ambatar sunanta a matsayin wacce za ta iya gadonsa.
A 'yan makonnin nan ta dauki gabaran aikin tsauraron sakonni ga Koriya Ta Kudu, kuma ta zama sabuwar wacce ake samun bayanai daga wajenta kan dangantaka tsakanin kasashen na Koriya.
Sai dai cukumurdar siyasar Koriya Ta Arewa abu ne mai wahalar ganewa cikin sauki.
Don haka da wuya a iya gano irin karfin iko da fada a ji da matashiyar mai shekara 32 take da shi.