Yakin Yemen: An cire sunan Saudiyya daga wadanda ayyukansu ke cutar yara

Kungiyoyin kare hakkin bil'adam sun soki Majalisar Dinkin Duniya MDD kan cire Rundunar sojin hadaka da Saudiyya ke jagoranta da ta yi daga jerin wasu sassa da ayyukansu ke cutar da ƙananan yara.

A wani rahoto tun farko da MDD ta fitar, ya gano yadda dakarun taron dangin suka hallaka ko jikkata ƙananan yara fiye da 200 a bara a yakin da take da mayakan Houthi a Yemen.

Babban Sakataren Majalisar, Antonio Guterres ya ce an samu matuƙar raguwar mutanen da ke mutuwa ko jikkata saboda hare-hare ta sama.

Kungiyoyin kare hakkin bil'adam sun soki Mista Guterres da banzatar da hujjojin da suke nuna keta hakkoki da aka yi.

Yaƙin da aka shafe shekara biyar ana wanda ya daidata Yemen, ya yi sanadin mutuwar nutun 100,000, ya kuma jawo mutane sun shiga halin ƙa-ƙa-ni-ka-yi mafi muni da aka taba samu a duniya.

Rahoton Sakatare Janar na MDD da ya gabatar ga kwamitin tsaro a kan yara da rikice-rikicen masu tada kayar baya ya ce an tabbatar da take dokar cin zarafin yara 2,159 sau 4,042 a yakin Yemen.

A jumulla a kalla yara 395 ne suka mutu ka kashe sannan yara 1,447 suka jikkata.

An alakanta mutuwa ko jikkatar yara 312 da ayyukan mayakan Houthi, 222 ga ayyukan rundunar sojin hadaka da Saudiyya ke jagoranta, 96 ga rundunar sojin hadaka da gwamnatin Yemen ke goyon baya, 51 ga mayakan sa kai, biyar ga kinhiyar al-Qaeda a yankin Larabawa sai kuma biyu ga kungiyar IS.

Kungiyoyin kare hakkin bil'adam sun ce wannan matakin na MDD na iya sanya yara cikin masifar wasu hare-haren.