Kusan mutum 200 aka kashe a Katsina da Borno a makon da ya gabata

    • Marubuci, Mustapha Musa Kaita
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Journalist

Tun daga ranar Lahadi, 7 ga watan Yunin 2020 zuwa ranar Asabar, abubuwa da dama muhimmai sun faru a Najeriya kuma sun ja hankulan 'yan kasar.

Mun tsakuro muku muhimmai daga cikinsu.

'Yan Boko Haram sun kashe mutum 90 a Borno, 'Yan bindiga sun hallaka sama da 100 a Katsina

..

Asalin hoton, Getty Images

A makon da ya gabata ne aka samu rahotanni daga jihohi biyu na arewacin Najeriya kan cewa an kashe farar hula kusan 200 a hare-haren da aka ƙaddamar kan al'ummomi a jihohin Borno da Katsina.

A arewa maso gabashin kasar, waɗanda lamarin ya faru kan idanunsu sun ce mayakan 'yan kungiyar ISWAP - wani tsagi na Boko Haram sun kutsa kauyen Gubio inda suka buɗe wa jama'a wuta har suka kashe mutum 69, sai dai a wata sanarwa da IS din ta fitar, ta yi iƙirarin kashe mutum 90.

A yankin arewa maso yammacin ƙasar, mazauna yankin sun shaida wa BBC cewa an kashe mutum fiye da 50 a hare-haren 'yan bindiga a ƙauyen Ƙadisau da ke ƙaramar hukumar Faskari ta jihar Katsina, sa'annan daga baya aka kai hari a garuruwan 'Yan kara da Faskari da 'Yan Tumaki da Dan Ali inda aka kashe sama da mutum 50.

Bayanan nan kuma 'yan bindigan sun je garin Mazoji a jihar ta Katsina inda suka kashe Mai Garin.

An yi zanga-zanga kan tabarbarewar tsaro a Katsina

..

Asalin hoton, UGC

A makon da ya gabata ne mazauna ƙauyen 'Yantumaki da ke jihar Katsina a arewacin Najeriya suka gudanar da zanga-zanga kan taɓarɓarewar tsaron da yankin ke fama da shi.

Hotunan da aka wallafa a shafukan intanet sun nuna masu zanga-zangar da safiyar ranar Talata inda suka hau kan tituna suna kokawa kan yadda gwamnatocin tarayya da na jihar suka zura ido kan yadda ɓarayi da 'yan bindiga ke cin karensu ba babbaka.

Bayanai sun nuna cewa matasan yankin sun harzuka ne bayan wasu 'yan bindiga sun kai hari a kauyen da safiyar ranar Talata inda suka sace wani malamin asibiti da diyarsa.

Matasan sun rika kona tayoyi da kuma allunan jam'iyyar APC mai mukin jihar don nuna rashin jin dadinsu game da rashin tsaron.

An yi bikin Ranar Dimokradiyya a Najeriya

..

Asalin hoton, Nigeria Presidency

A wannan makon ranar 12 ga wata aka yi bikin Ranar Dimokradiyya a Najeriya, kuma a jawabinsa na ranar, Shugaba Muhammadu Buhari ya gode wa ƙasar bisa jajircewarsu wurin kafuwar dimokuraɗiyya.

Ga kaɗan daga cikin abubuwan da shugaban ya faɗa a ranar:

  • Yan bindiga sun yi amfani da dokar kulle a Katsina da Borno, inda suka kashe mutane da dama
  • Annobar korona na kawo wa dimokraɗiyyar Najeriya barazana
  • Gwamnatin Tarayya za ta samar wa mutum 774,000 aikin yi - 1,000 a kowace ƙaramar hukuma a Najeriya
  • 'Yan jarida ne madubin al'umma kuma "na gode musu kan tabbatar da dimokuraɗiyya a Najeriya"

APC ta hana Godwin Obaseki takara

..

A ranar Juma'a ne kwamitin da ke tantance 'yan takara na jam'iyyar APC a jihar Edo ya haramta wa gwamnan jihar Godwin Obaseki shiga zaɓen fitar da gwani wanda za a gudanar kafin tsayar da ɗantakarar gwamna.

Shugaban kwamitin, Jonathan Ayuba ne ya bayyana hakan yayin da ya ke bayar da rahoton ayyukan kwamitin ga shugaban jam'iyyar APC Adams Oshiomhole.

Ya bayyana cewa an haramta wa Obaseki tsayawa takarar ne sakamakon matsalar da ake ganin akwai tattare da takardun makaranta na gwamnan.

Sai dai a wani ɓangaren kuma, kafofin yaɗa labarai na Najeriyar sun ruwaito cewa Mista Obasekin ya ce ba zai ɗaukaka ƙara ba.

El-Rufai ya sassauta dokar hana fita

...

Asalin hoton, @GOVKADUNA

A ranar Talata ne gwamnatin Kaduna da ke arewacin Najeriya ta sassauta dokar kullen da ta saka a jihar wadda ake kallo a matsayin mafi tsauri a arewacin kasar.

Gwamna Nasir Ahmed El-Rufai ne ya sanar da hakan a wani jawabi da ya yi ga jihar inda ya ce a karon farko cikin makonni masu yawa za a bar masallatai su yi Sallar Juma'a sannan majami'u su gudanar da ibada ranar Lahadi.

Gwamnan ya kuma sassauta dokar hana zirga-zirga a jihar amma a yanzu babu fita daga ƙarfe 8:00 na dare zuwa 5:00 na asuba.

Sai dai gwamnan ya ce ba za a bude kasuwanni ba tukunna.