Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kathy Sullivan: Matar da ta je sararin samaniya da kuma ƙarƙashin teku
- Marubuci, Daga Pooja Chhabria
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
Wata tsohuwar 'yar sama-jannati ta zama mutum ta farko da ta je sararin samaniya da kuma can karkashin teku.
Dakta Kathy Sullivan ta kafa tarihin tattakin da ta yi da kafarta na sawu 35,810 a cikin teku ranar Lahadi.
"Na ji ni kamar wata bakuwa a wata duniya da kuma tsallake watan da na yi kamar wata iyakar kasa. Ba karamin abin farin ciki ba ne," in ji 'yar shekara 68 din kamar yadda ta shaida wa BBC.
Ta zama ta takwas cikin jerin wadanda suka taba zuwa, kuma mace ta farko da ta taba zuwa karshen karkashin teku, yana kai kilomita 11 daga samar ruwan teku kafin aje karkashin tekun.
Dakta Sullivan ta shafe kimanin sa'a daya da rabi tana neman hanyar da za ta bi ta je kasan ruwan ta cikin wata na'ura, wadda aka haɗa domin jurewa hanƙoron ruwan teku.
Wanda ya fara zuwa teku daban-daban har biyar Victor Vescovo ya yi wa Sullivan rakiya.
"Bai taba zuwa raina ba cewa wata rana zan samu irin wannan damar, ko kuma Victor zai neme ni muje tare," in ji Dakta Sullivan.
A kasar hanyoyin cikin tekun kamar Mariana, ruwan ya zama kankara, ga shi babu haske ko kadan, kuma ɗumin ruwan yana karuwa sosai tare da diddiga.
A shekarar 1960 aka fara zuwa can kasan tekun, kuma wani sojan ruwan Amurka Laftanal Don Walsh da wani Injiniyan Switzerland Jacques Piccard, ne suka je ta wata tashar jirgin ruwan da ake kira Bathyscaphe.
Wani mai shirya fina-finai James Cameroon ne ya kirkiri wani kayan shiga ruwan da su, tsawon rabin karni kenan a 2012.
Amma an kirkiri sabbin kayan da za a rika sakawa ana zuwa kasan tekun da su daga baya.
Sullivan ta zama 'yar sama jannati ne a 1979 kuma ta kafa tarihin zama macen farko 'yar Amurka da ta fara zuwa duniyar wata a 1984.
Ta kuma shafe sama da sa'a 532 a sararin samaniya kuma a 2004 ta kafa tarihin zama 'yar sama-jannatin da ta fi kowa shahara.
Daga baya ta hade da kungiyar masu zuwa samaniya da ta masu zuwa cikin teku, wadda daga baya kuma ta shugabance ta.
A wata hira da ta yi da BBC ta waya, lokacin da take cikin tekun, Dakta Sullivan ta bayyana teku da samaniya a matsayin "wasu manyan abubuwan tarihi da aka samar tun kafin halittar dan adam".
Yanzu ita ce mutum ta farko da ta je duka yankunan biyu, cikin yanayin da duka suka sha bamban da juna.
"Na samu horo biyu ne na kwararriya a kimiya da kuma injiniya don haka ina da kwarewar sarrafa na'urorin da ake zuwa duniyoyin biyu da su," ta bayyana.
"Sun zamar min kamar wata shinfiɗa da ke ba mu damar zuwa wuraren da dan adam baya iya zuwa in babu su."
Kafin zama 'yar sama-jannati Dakta Sullivan ta gama karatun digirinta na uku a jami'ar Dalhousie inda suka rika ziyartar teku daban-daban da kuma zane-zanensu.
Yayin da damar zuwa karkashin ruwa ta zo nan da nan Dakta Sullivan ta amsheta hannu biyu.
Rob Mccallum shi ne ya kirkiri wata kungiya ta masu shiga ruwa WYOS ya ce, " Tana da kwarewar da ake nema wajen amfani da na'urorin da ake aikin da su."
Bayan sun kammala tafiyarsu Dakta Sullivan da Victor sun kira hukumar da ke kula da tashar sararin smaaniya daga kimanin kilomita 400 gaba da guniyar nan da muke ciki.
"Kamar sake gamuwa da wanda ka dade baka gani ba ne."
"Sama da gwamman shekaru ina daukar kaina a matsayin 'yar sama jannati, masaniyar kimiyya kuma mai bankado sabbin ilimmai."
"Ina fatan sanya wa wasu jin suna da sha'awar bankado abin da yake boye, da kuma yadda za a ci gaba da fito da wasu sabbin wurare da ke wajen duniyar nan tamu."