Yadda hankula suka tashi bayan samun gawar wata budurwa a rataye a Afirka ta Kudu

Tshegofatso Pule

Asalin hoton, @Keba99

Bayanan hoto, An gano gawarta rataye a wata bishiya bayan an sassara ta a Johannesburg
Lokacin karatu: Minti 2

Maudu'i mai taken #JusticeForTshego a turance, wato a yi wa Tsego adalci, yana ci gaba da jan hankula a shafin Twitter a Afirka ta Kudu, sakamakon kisan da aka yi wa wata budurwa mai shekara 28, Tshegofatso Pule.

An gano gawarta rataye a wata bishiya bayan an sassara ta a Johannesburg.

Kafofin watsa labaran kasar sun ambato 'yan sanda na cewa tana dauke da cikin wata takwas lokacin da aka kashe ta.

Jaridar Sowetan ta bayar da labarin cewa Ms Pule ta ɓata a makon jiya amma daga bisani an gano gawarta a rataye.

Ta ambato mai magana da yawun rundunar 'yan sanda Kyaftin Kay Makhubele na cewa an soma gudanar da bincike kan kisan budurwar.

Ana ci gaba da samun rahotannin kashe mata a Afirka ta Kudu kuma a bara Shugaba Cyril Ramaphosa ya ce kasar tana "cikin kasashen da mata suka fi fuskantar barazanar kisa a duniya".

Alkaluma kan aikata laifuka da aka fitar a kasar a bara sun nuna cewa mata baligai 2,930 aka kashe a tsakanin wata 12 daga shekarar 2017 zuwa 2018, abin da ke nufin ana kashe mace daya cikin ko wadanne awa uku a kasar.

A shafin Twitter, mutane suna ta yin kira ga 'yan sanda su tabbatar sun kamo duk wanda ya kashe Ms Pule, ko da yake sun kuma nuna shakku kan kwarewar 'yan sandan ta gano masu laifukan.

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

Presentational white space
Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2

Presentational white space

A shekarar da ta wuce, al'ummar kasar sun yi zanga-zanga sau da dama bayan an samu yawaitar rahotannin kisan mata inda suka rika kira a dauki karin matakan magance matsalar.

Tun lokacin da aka kaddamar da kotuna na musamman kan zargin yi wa mata fyade - sun yi ta fama da matsalar rashin kudi, a cewar wakiliyar BBC a Johannesburg, Pumza Fihlani.

Presentational grey line