An ceto Baturen da ya kwana shida cikin rijiya a Indonesia

An ceto wani Baturen Burtaniya da ya faɗa wata rijiya da ke tsibirin Bali na ƙasar Indonesiya, bayan shafe kwana shida a cikinta.

Jacob Roberts ya karye a ƙafa bayan da ya faɗa rijiyar mai zurfin mita huɗu a lokacin da yake gudu sakamakon bin sa da kare ya yi, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ambato mahukuntan yankin sun faɗa.

Rijiyar ta ƙafe babu ruwa a cikinta, amma karayar da ya samu a ƙafarsa ce ta hana shi fita. Shaidu sun ce akwai ruwa ƙaɗan a cikin rijiyar da ya taimaka masa wajen rayuwa.

Ihun neman ceto da Mr Roberts ya dinga yi ne ya jawo hankalin wani mazaunin wajen.

Mutumin na neman wajen da zai kai dabbobinsa su yi kiwo ne a kusa da wajen, wanda ya kasance keɓaɓɓen waje ne a cikin ƙauyen, kamar yadda wani kamfanin yaɗa labarai Bali Sun ya ruwaito. Daga nan sai ya sanar da hukumomin wajen.

"Ya yi zuru-zuru ya rame sannan ya ji rauni,'' kamar yadda shugaban 'yan sandan Kudancin Kuta, Yusak Agustinus Sooai ya ce a lokacin da yake bayani kan yanayin da aka same shi bayan gano shi a ranar Asabar.

Shugaban tawagar masu aikin ceto ta yankin Gede Darmada ya ce an ɗauko Mr Roberts ne daga cikin rijiyar inda maza uku suka ɗora shi a kan gadon ɗaukar marasa lafiya, kamar yadda kungiyar agajin ta Basarnas Bali ta ce.

A wata sanarwa a shafin Instagram, kungiyar Basarnas ta ce an kai Mr Roberts asibitin BIMC Nusa Dua.

Ƙauyen Pecatu yana kusa ne da fitaccen wajen yawon buɗe ido na Nusa Dua da ke kudancin Bali.

Babu tabbas kan ko Mr Roberts mazaunin wajen ne ko ɗan yawon buɗe ido ne.

Bali ta shafe watannin cikin dokar kulle sakamakon annobar cutar korona, sai dai a yanzu haka ana ci gaba da buɗe wurare da dama cikin yin taka tsan-tsan.