'Zawarawana 1,600 duk da nakasata'

Shin ko kun taba samun labarin bazawarar da take da manema fiye da dubu?

Matar mai larurar rashin kafa mai shekara 25 ta ce ta kasa zabar mutumin da za ta aura saboda yawan masu zuwa wurinta.

Matar ta ce tun bayan da aurenta na fari ya mutu, ta fuskanci tana samun matsala na mijin da zata aura, ma'ana idan mutum ya fito zai aureta wani sai iyayensa suki suce zai kawo musu mai nakasa.

Ta ce wani kuma haka kawai sai wani abu ya gindaya a fasa auren.

Bazawarar ta ce daga nan ne sai ta samu littafi ta fara rubuta duk wanda yazo wajenta da neman aure.

Ku saurari hirar da BBC tayi da ita: