Coronavirus: Hotunan yadda aka bude manyan masallatan Madina da Ƙudus

Asalin hoton, Getty Images
An buɗe biyu daga cikin manyan wuraren ibadar Musulmi bayan kusan wata biyu da kulle su sakamakon annobar cutar korona, inda mutane suka shiga cikin tsauraran matakan kariya.
Ɗaruruwan Musulmai ne suka yi wa Masallacin Ƙudus tsinke, wanda ake kira da Al-Aqsa a birnin Ƙudus domin yin sallar Asuba. Shi ne massallaci na uku mafi tsarki a addinin Musulunci.
Wasu sun riƙa yin kabbara, yayin da wasu kuma suka riƙa sumbatar dandariyar ƙasar masallacin.
An ɗauki matakan rage yaɗuwar cutar a cikin masallacin.

Asalin hoton, Reuters
An duba yanayin zafin jikin masallatan sannan suka bai wa juna tazara a sahun sallar. Kazalika an umarce su da su saka takunkumi tare da zuwa da shimfiɗar sallarsu.
"Na ji kamar rayuwata ce ta dawo da aka buɗe masallacin. Godiya ta tabbata ga Allah, a cewar wani mai suna Umm Hisham cikin shauƙi, yayin da yake shiga masallacin.

Asalin hoton, Getty Images
Masallacin Al-Aqsa da ma sauran wurare masu tsarki sun kasance a garƙame tun daga tsakiyar watan Maris, hatta a watan Ramadana ba su samu damar yin sallolin tarawihi (asham) a cikinsu ba.
Duk da cewa har yanzu akwai barazanar annobar ta korona, wasu ƙasashe suna sassauta dokar kullen sannu a hankali tare da ƙayyade adadin waɗanda za su shiga cikin wuraren ibadar.

Asalin hoton, EPA
A ranar Lahadi ma an samu irin wannan cikowar a Masallacin Annabi na Madina, inda mutane suka taru domin yin sallah.
Masallacin na daga cikin kusan 90,000 da Saudiyya ta shirya buɗewa.
Kafin a buɗe shi, an tura wa miliyoyin mazauna ƙasar sakon tes ɗauke da sabbin ƙa'idojin gudanar da ibada.

Asalin hoton, Reuters
Saƙonnin tes ɗin da aka tura wa jama'a sun neme su da su bai wa juna tazarar mita biyu (ƙafa 6.5) sannan kuma kada su gaisa ta hanyar musabaha ko kuma rungumar juna.
Kazalika an faɗa musu cewa su ci gaba da wanke hannu a gida kamar yadda aka saba saboda ba za a buɗe wurin yin alwala na masallacin ba.

Asalin hoton, Reuters
Ba za a riƙa wuce minti 15 ba yayin gudanar da sallolin.
Masallacin harami na Makkah zai ci gaba da kasancewa a rufe har illa Masha'Allahu. Masallacin da ya fi kowanne tsarki, yana karɓar baƙuncin miliyoyin mutane duk shekara domin aikin Hajji da Umara.
Dukkanin hotunan akwai waɗanda suka mallake su











