'Trump bai aika wa Najeriya na'urorin taimakawa mutum yin numfashi ba'

Trump

Asalin hoton, Getty Images

Ministan watsa labaran Najeriya ya ce har yanzu kasar ba ta karbi na'urorin taimakawa masu dauke da cutar korona yin numfashi ba, wadanda shugaban Amurka Donald Trump ya yi alkawarin bai wa kasar a watan Afrilu.

Lai Mohammed ya musanta kalaman da Mr Trump ya yi makon jiya cewa ya aike da na'urorin 1,000 ga Najeriya.

Ya kara da cewa gwamnatin Najeriya za ta sanar da zarar na'urorin sun isa kasar.

Shugaba Trump ya yi alkawarin aikawa da na'urorin taimakawa mutane yin numfasin ne lokacin da suka yi wayar tarho da Shugaba Muhammadu Buhari ranar 28 ga watan Afrilu. Ya ce gwamnatin Amurka tana son taimakwa Najeriya wajen yaki da cutar korona.

Makon jiya, lokacin da ya ziyarci kamfanin motoci na Ford da ke birnin Michigan, Mr Trump ya ce kasarsa ta aike wa Najeriya na'urori 1,000.

Ya zuwa yanzu, an tabbatar mutum 8,915 sun kamu da cutar korona a Najeriya, inda mutum 259 suka mutu.

A wannan makon, kungiyar likitoci ta kasar ta ce mutanen da suka kamu da cutar korona sun ninka sau hudu a kan yadda ake sanarwa.

Lai Mohammed

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Lai Mohammed ya ce da zarar na'urorin sun iso za a sanar