Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mulkin Buhari: Shin kwalliya ta biya kudin sabulu?
A Najeriya, a yau 29 ga watan Mayu ne shugaban kasar Muhammadu Buhari ke cika shekara daya da sake hawan karagar mulki, bayan zaben da aka sake yi masa domin wa`adin mulki na biyu.
Shugaban kasar dai ya yi alwashin ci gaba da aiwatar da ayyukan alheri tare da gyara kura-kuran da ya yi a baya.
Ya 'yan Najeriya ke kallon tafiyar gwamnatin zuwa yanzu?
A bara wajen bukin ranar demokuradiyya ta kasar, wanda aka yi 'yan kwanaki kadan bayan ya sha rantsuwar kama aiki, bayan an sake zabar sa a matsayin shugaban kasa karo na biyu, shugaba Buhari ya yi alkawari ga 'yan kasar:
"Babban aikin da ke gaban wannan sabuwar gwamnatin shi ne tabbatar da an kammala ayyukan da muka fara shekaru hudu da suka gabata."
Kuma wajen ne ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa ta dogewa a kan akidoji da manufofin da yace an san ta da su, musamman ma dorawa a kan inda ta tsaya a wa'adin mulki na farko wajen inganta tsaro da bunkasa tattalin arziki da kuma yaki da cin hanci da rashawa.
Gwamnatin APC mai mulkin Najeriyar, karkashin jagorancin shugaba Buhari na ikirarin cewa taka rawa a bangaren tsaro, kasancewar ta karya-logon mayakan Boko Haram, sannan ta aiwatar da wasu manufofin da suke taimakawa wajen bunkasa tattalin arziki, bayan nasarar da take ikirarin samun wajen yaki da rashawa.
Amma ra`ayoyin wasu `yan Najeriyar na nuna cewa sun kosa da gwamnatin.
Alhaji Buba Galadima, jigo a tsakanin 'yan adawar Nijeriya ya ce bai ga wani abin yabawa ba.
A bangaren tsaro, Buba Galadima ya ce "A zamanin Jonathan, inda ake fama da rashin tsaro, har yayi kauri shi ne Borno da Yobe da Adamawa sai kuma inda ba a rasa ba. Amma a yau a koma ma mahaifar Janar Buhari Katsina, yanzu kai ka je Batsari ko Kankara ko Dutsinma ko Danmusa ko Jibiya kace da su akwai tsaro?"
BBC ta kuma nemi ra'ayoyin wasu 'yan Najeriya a Abuja babban birnin kasar:
Wannan wani mazaunin unguwar Wuse ne da ke tsakiyar birnin: "Gaskiya ni magoyin bayansa ne sosai sai dai ance Juma'ar da za tayi kyau daga Laraba ake ganewa. Mu mun kasa gane inda aka dosa a gwamnatin nan."
Da aka tambaye shi ko zai sake zaban Shugaba Buhari idan ya sake tsaya wa takara, sai ya ce, "Gaskiya ba zan iya sake zaban shi ba."
Wani malamin na daban kuma shi ma ya ce a da shi "dan a mutu na Buhari ne", amma yanzu ba wani abin da ya ce ya gani a kasa illa, "nusiba da bala'i da muke ciki".
`Yan magana kan ce inda aka ki ka da kwana, wani kan so ka da shekara! Wasu 'yan Najeriyar na ganin alfanun gwamnatin shugaba Buharin.
Ban taba samun wata gwamnati da take taimaka wa masu karamin karfi domin su tsaya da kafafuwansu kamar gwamnatin Buhari ba, Ni manomi ne, kuma ina jin dadin irin taimakon da yake bayar wa a bangaren noma."
Abubuwa da dama sun faru a wannan shekara guda da shugaba Buhari ya yi bayan sake zabarsa da aka yi, kuma wasu sun dadada wa `yan kasar, yayin da wasu kuma aka samu akasi, ciki har fara biyan ma`aikata albashi mafi kankanta na naira dubu talatin, da kumamatakin da gwamnati ta dauka na rufe iyakokin kasar da ke tudu da nufin hana fasa-kwauri.
Akwai kuma takun-sakar da kungiyar malaman jami'a ke yi da gwamnati, sakamakon zarginta da gazawa wajen cika alkawari.
Har wa yau, a cikin shekarar ne aka yi ta nuna yatsa tsakanin wasu mukarraban shugaban kasar, inda aka ga mai baiwa shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro na zargin marigayi shugaban ma`aikatan fadar gwamnati Mallam Abba Kyari da yin shisshigi a aikinsa.
Irin kalaman da ke fitowa daga bakin `yan Najeriya da dama, na nuna cewa sai gwamnati ta yi da gaske kafin ta burge su.
Ga abin da Buba Galadima ke cewa a bangaren yaki da cin hanci da rashawa da gwamnatin Shugaba Buhari ke ikirarin samun nasarori a kai:
"Gwamnoni wadanda suka saci kudin al'umma, kowa ya san wani wanda ya saci kudin al'umma biliyan 300, kowa ya san shi, amma da ya shiga APC sunansa Muhammad har minista ya zama."
Sai dai sabanin yawaita bulaguro zuwa kasashen waje da shugaba Buhari ya yi a cikin shekaru hudun da suka wuce, a wannan shekarar siyasa mai karewa, shugaban kasar ya shafe kusan rabinta ne yana zaman gida.
Abin da ba a sani ba shi ne ko annobar korona ce ta takaita masa tafiye-tafiyen, ko kuma wani sabon salon takun mulki ne.