Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus a Najeriya: 'Masu cutar sun ninka sau huɗu kan yadda ake sanarwa'
Kungiyar likitoci ta Najeriya ta ce akwai yiwuwar masu dauke da cutar korona a kasar sun nunka sau hudu kan adadin da hukumomi irin su hukumar yaki da dakile cutuka masu yaduwa, NCDC, suka sanar.
Ya zuwa ranar Laraba dai, NCDC ta ce mutum 8,733 ne suka harbu da cutar, yayin da mutum 2501 suka warke, sannan mutum 254 suka mutu.
Sai dai shugaban kungiyar likitocin Najeriya, Francis Faduyile, ya shaida wa BBC cewa suna jayayya game da sahihancin wadannan alkaluma.
Ya ce: "Mun damu saboda alkaluman da aka sanar sun gaza kwarai da gaske da hakikanin alkaluman da muka sani ko wadanda muka sa rai za a sanar. A halin da ake ciki, mun san cewa ba mu da kasa da ninki hudu na ilahirin alkaluman da aka fitar...
Akwai mutane da dama da suka nuna alamar suna dauke da Covid-19 amma suna jira kwana uku zuwa biyar kafin a sanar da sakamakon gwajinsu. Don haka akwai masu cutar da dama da ba a sanar da sakamakonsu ba."
Da ma dai an dade ana fargabar cewa akwai mutane da dama da suke mutuwa sakamakon kamuwa da abin da aka ce bakuwar cuta ce a jihar Kano da ke arewacin kasar, ko da yake wasu na ganin cutar korona ce take kashe su.
Masu haka kaburbura a makabartu sun bayyana cewa gawarwakin da ake kai musu sun zarta yadda suka saba gani a irin wannan lokaci a shekarun da suka gabata.
Wani kwamiti da gwamnatin tarayya ta aika jihar ta Kano da wasu jihohin arewacin kasar yana gudanar da bincike kan lamarin, kuma ya ce sun gano dalilai bakwai da ke suka haddasa mutuwar mutanen.
Wani likita Nicaise Ndembi, wanda yake aiki a cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa ta Afirka, ya ce yana fargabar cutar korona za ta yadu daga Kano zuwa makwabtan jihohi.