El-Rufai: 'Zan ɗaure iyayen da suka kai 'ya'yansu almajiranci'

Gwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya bayyana cewa daga yanzu za a riƙa hukunta iyayen da suka kai 'ya'yansu makarantar allo a jihar.

Gwamnan ya bayyana cewa duk malamin da ya karɓi yara a matsayin almajirai a makarantar allo za a ɗaure shi ko kuma a ci tararsa daga naira dubu 100 zuwa 200.

El-Rufai ya bayyana haka ne ranar Litinin yayin wata ziyara da ya kai wata cibiya da aka killace tare da kula da almajirai kusan 200 da aka mayar da su Kaduna daga Jihar Nassarawa a Kurmin Mashi da ke birnin Kaduna.

El-Rufai ya koka kan cewa duk almajiran da aka ɗebo daga wasu jihohi 'yan Kaduna ne, yana mai cewa jihar na da alhakin ba su duk wani taimako da suke buƙata domin ci gabansu.

"Saboda haka za mu ci gaba da karɓar almajirai 'yan Kaduna domin kula da su sannan mu saka su a makarantu na zamani kusa da inda iyayensu ke zaune," in ji El-Rufai.

Da ma can El-rufa'i ya yi ta nanata cewa mafi yawan masu cutar korona a jiharsa almajiran da Gwamna Ganduje ya mayar da su ne daga Kano, abin da ya sa ake ganin kamar hakan ya jawo zaman doya da manja tsakanin shugabannin biyu.

Jihar Kaduna na da mutum 189 da suka harbu da cutar korona ya zuwa daren Litinin, a cewar hukumar yaki da cutuka masu yaduwa, NCDC, yayin da biyar suka mutu da kuma 116 da suka warke.