Najeriya ba ta da kuɗin da za ta shigo da abinci daga ƙasashen waje - Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce dole manoman a kasar su kara dukufa wajen noma isasshen abincin da zai wadatar da kasar, saboda gwamnati "ba ta da kudin da za ta iya shigo a abinci daga wajen."

Shugaba Buhari ya ba da wannan shawarar ne lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a fadar gwamnatin kasar bayan idar da sallar Idi.

Bayanin nasa na zuwa ne lokacin da ake ci gaba da nuna damuwa kan karancin abinci da ake fama da shi a wannan lokacin a annobar korona, da kuma tashin farashin kayan abincin a kasar mafi yawan jama'a a Afrika.

A cewar Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya, tun kafin annobar korona manoma ba sa iya samar da abincin da zai ciyar da al'ummar kasar miliyan 200.

Ko da yake noma shi ne babbar sana'ar da 'yan kasar suka fi yi, amma gwamnatoti daban-daban sun yi watsi da shi inda suka mayar da hankali kan man fetur wanda kasuwarsa ta yi muguwar faduwa saboda annobar korona.

Gwamnatin Shugaba Buhari ta dade wajen bunkasa aikin gonan shinkafa inda ta rika yi wa masu shigo da shinkafa 'yar Thailand ta hanyar fasa-kauri dirar mikiya sannan ta rufe iyakokinta.

Kafin wannan lokacin, Najeriya tana shigo da shinkafa fiye da tan miliyan daya daga Thailand duk shekara.

Yanzu tana bari a shigo da shinkafa 'yar-waje ne kawai ta hanyar iyakokin ruwanta - inda take sanya haraji mai yawa.

Farashin abinci ya yi matukar tashi a Najeriya tun da annobar korona ta barke kuma kudin shigar da ake samu daga man fetur ya yi matuar raguwa saboda farashinsa da ya fadi.

Asusun Bayar da Lamuni na Duniya ya yi hasashen cewa tattalin arzikin Najeriya zai tsuke da kashi 1.5 a 2020.