Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus: Za a iya barin tazara a sansanonin 'yan gudun hijra?
- Marubuci, Navin Singh Khadka
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Environment correspondent, BBC World Service
"Barin tazara ba zai yiwu ba idan mutanen da suka rasa muhallansu na rayuwa a sansanoni," in ji Marshal Makavure, jami'i a kungiyar IFRC ta Gabashin Afrika.
"An tursasa wa mutane karya dokokin Covid-19 saboda halin da suke ciki."
BBC ta yi Magana da mutanen da ke zaune a yankunan da ke fama da matsanancin yanayi.
Indiya
Subrat Kumar Padhihary, manomi mai shekaru 38 a jihar Odisha da ke Indiya ya damu.
Hukumomin Indiya na zaman dar-dar yayin da ake sa rai Guguwar Amphanm, wadda za ta fada Yammacin Bengal da Odisha ranar Laraba, za ta habaka ta zama guguwa mai karfin gaske.
Kauyen sy Subrat na da nisan kusan kilomita 40 daga teku. Gidansa da yake zaune da matarsa da 'ya'yansa mata uku da mahaifiyarsa ya yi matukar lalacewa dalilin Guguwar Fani a bara, don haka ba ya tunanin a yanzu gidan zai jure Guguwar Amphan.
Subrat na ganin wannan za ma ta fi hadari.
"Fargabata it ace za a kai mu makarantu da ke kusa da aka riga aka mayar da su cibiyoyin kula da masu Covid-19.
"Babu cibiyoyi da yawa a kauyenmu, kuma wannan na nufin za mu koma muna zama tare da mutanen da ake tunanin suna dauke da cutar Covid-19."
"Jihar Yammacin Bengal ta dade tana fama da masu dauke da cutar korona kuma abin damuwa ne yadda ba a shirya wa wannan guguwar ba," a cewar Siddarth Srinivas, wani jami'in kungiyar Oxfam a Asiya.
A baya, wasu jihohi a Indiya sun ceci mutane ta hanyar ajiye su a makarantu da gine-ginen gwamnati amma wannan karon hakan ba zai yiwu ba saboda annobar nan."
Uganda
Yankin Kasese a yammacin Uganda na daya daga cikin wuraren da ambaliyar ruwa ta fi lalatawa kuma daruruwan mutane ambaliyar ta daidaita.
Joseline Kabugho na da ciki wata shidda. An tursasa wa mai shekaru ashirin da ukun da yaranta biyu zama a daya daga cikin makarantun da aka mayara sansani a yankin.
Tana zaune ne a sansanin duk da cewa juna biyun da take da shi na nufin tana cikin hadarin kamuwa da cutar korona. Akwai kusan mutum 200 da suka rasa muhallansu tare da ita a sansanin.
""Muna cikin wani hali yanzu," a cewarta, inda take zaune tare da wasu iyalai uku. "Ba zan iya ware kaina in zauna ni kadai ba saboda karancin wurin zama.
"Ina fargabar kamuwa da cutar korona, kuma na damu saboda 'ya'yana da dan da ke cikina," ta shaida wa BBC.
Joseline na bacci a gefen 'ya'yanta biyu a daren 7 ga watan Mayu, lokacin da ta jiyo sauran mutanen kauyensu na ta kwarma ihu.
"Daga baya na fahimci ashe ce min suke yi in gudu. Ambaliyar ruwa ta mamaye gaba daya kauyen.
"Na sunkuci 'ya'yana biyu na ruga da gudu, ban samu lokacin daukar komai na."
Ta yi wa dan da ke cikinta sayayya kafin ambaliyar ruwan. "Ko wadannan kayan ban iya daukowa ba. Ambaliyar ta tafi da su.
"Duk wani abu da muke da shi ambaliyar ta tafi da shi."
Mijinta na aiki ne a wani yankin na daban kuma ya kasa zuwa inda ta ke saboda dokokin hana zirga-zirga saboda cutar korona. "Ba ni da inda za ni kuma ban san abin da zan yi ba nan gaba."
Ma'aikatan agaji na Red Cross sun ce a halin yanzu dubban mutane ne ke neman mafaka a coci-coci da makarantu a Gabashin Afrika da ambaliyar ruwa ta yi wa ta'asa kuma inda suke da karancin ruwa da sabulun wanke hannu.
Daruruwa sun mutu kuma dubbai sun rasa muhallansu saboda ambaliyar ruwan a sama da kasashe shidda.
Sama da mutum 2,700 ne cutar korona ta kasha kuma kusan mutum 82,000 ne suka kamu da cutar a afrika, a cewar Jami'ar John Hopkins.
Cikin kasashen da ambaliyar ta shafa a Gabashin Africa, Somaliya ce ta fi yawan mutanen da suka mutu inda ta rasa mutum 55 sai Kenya ta rasa mutum 50 yayin da Tanzania ta rasa mutum 21.
Tsibirin Pacific
Guguwar Harold ta fada kasashen da ke tsibirin Pacific fiye da wata daya da ya wuce.
Sai da wasu kasashen suka dage dokokin hana zirga-zirga don bai wa mutane damar neman mafaka a sansanoni. Har yanzu akwai mutane a sansanonin saboda annobar ta hana ayyukan agaji ci gaba.
Kasar da guguwar ta fi shafa, Vanuatu, ta tsawaita dokar ta baci saboda mutum 92,000 da guguwar ta shafa a cewar asusun kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF.
A kasar Fiji, kusan sansanonin ajiye wadanda suka rasa muhallansu 10 na aiki saboda har yanzu ba a gama gyagijewa daga barnar da guguwar ta yi ba.
"Har yanzu samun ruwan sha babban kalubale ne saboda guguwar ta lalata hanyoyin samun ruwa," a cewar vani Catanasiga, shugaban ma'aikatar ayyukan jin kai a Fiji.
"Idan babu ruwa, bin dokokin kula da lafiya na Covid-19 zai yi wuya, duk da cewa gwamnatin Fiji ta yi nasarar shawo kan annobar."
Kungiyoyin agaji sun ce ayyukan agaji na iya taimakawa wajen bin dokokin Covid-19.
Ma'aikaciyar agaji a Red Cross Irene Nakasiits na rarraba ruwa da sabulu ga al'ummun da ambaliyar ruwa ta shafa a Yammacin Uganda.
"Duk da cewa babban kalubale ne yin haka, muna iya tunatar da al'ummun da ambaliyar ta shafa su bi ka'idojin," a cewar Marshal Mukuvare na IFRC.
"Muna iya rubuta sakonni kan abinci da sauran kayan agaji, wanda muke rabawa a wuraren da abin ya shafa.
"Wannan na taimakawa mutane."
Ba abu ne da aka saba gani ba, a cewar Siddarth Srinivas jami'in Oxfam a Asiya. "Idan aka zo batum yadda za a shawo kan matsanancin yanayi da annoba kamar ta korona, yanzu ma aka fara batun.
"Sai an yi dogon nazari kafin a samu kwararan matakai."