Yaushe rikicin cikin gida zai ƙare a jam’iyyar APC?

Babbar jam'iyya mai mulki a Najeriya, APC ta sake tsunduma cikin wani rikicin shugabanci bayan nada Bulama Waziri a matsayin babban sakatarenta na kasa.
Lamarin dai ya bar baya da kura inda wani bangare na 'ƴan jam'iyyar ya ce bai lamunci nadin ba, sai dai a yi zabe kamar yadda tsarin mulkin APC ya tanada.
Tun bayan da tsohon babban sakataren jam'iyyar Mai Mala Buni ya bar kujerar shekarar da ta gabata lokacin da ya samu tikitin takarar gwamnan jiha, sai yanzu ne aka maye gurbinsa.
Sanata Lawal Shu'aibu wanda shi ne mataimakin shugaban jam'iyyar APC shiyyar arewacin kasar ne dai ya fito ya soki nadin Waziri Bulama, inda ya caccaki shugabancin Adams Oshiomole.
Me 'yan jam'iyyar APC ke cewagame da nadin Waziri Bulama?
Tun bayan sanar da nadin Waziri Bulama a matsayin baban sakataren jam'iyyar na rikon kwarya a farko wannan mako, wasu 'yan jam'iyyar irin su Sanata Lawal Shu'aibu, ke cewa "Nadin Waziri Bulama alamu ne na yadda APC ta fada halin rashin doka da oda."
A wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba mai taken "APC da Dorewar jam'iyyar, A yi taka-tsantsan", Sanata Shu'aibu ya ce " na ja hankalin Adams Oshiomole game da hatsarin da yake son jefa jam'iyyar APC a ciki.
Matuƙar aka tafi a haka to alamu na nuna jam'iyyar za ta fadi a zaben jihohin Ondo da Edo kasancewar ba a sanya gaskiya a tsarin fitar da 'yan takarar cikin gida ba.
Kuma hakan ya yi wa sashe na 20 na kundin mulkin jam'iyyar karan tsaye saboda haka akwai alamu ƙarara cewa jam'iyyar adawa ta PDP za ta kwace iko daga APC."
Jam'iyyar APC ta 'dare kan nadin Waziri Bulama'
Masu fashin baki a Najeriya irin su Dr Abubakar Kari, masanin kimiyyar siyasa wanda ya ce rikicin cikin gida a jam'iyyar APC ba sabon abu ba ne illa dai ya lafa ne amma yanzu ya kara tasowa wanda kuma ya nuna karara darewar jam'iyyar.
Ya ce "rikicin ya fara tun bayan saukar Mai Mala Buni inda aka nemi nada Waziri Bulama tun a wancan lokacin amma wasu 'yan jam'iyyar suka tayar da jijiyoyin wuya, abin da ya sa aka haƙura zuwa yanzu."
Dr Kari ya ce batun nadin Waziri Bulama ne ya so yin sanadiyyar tunbuke shugaban APC na kasa, Adams Oshiomole a 'yan makonnin da suka gabata kafin daga bisani a sasanta.
To sai dai masanin kimiyyar siyasar na Najeriya ya ce "sake bijiro da batun nadin ba komai zai haifar ba illa kara jefa jam'iyyar cikin irin wancan rikicin shugabanci da ta sha fama da shi.
Ya ƙara da cewa "komai zai iya faruwa da jam'iyyar."
'Kulle-kullen zaben 2023 ka iya rusa APC'
Dr Abubakar Kari ya ce daya daga cikin manyan dalilan da ke haifar da rikicin cikin gida a APC mai mulki shi ne "rashin mutunta tsarin mulkin jam'iyya inda ake hawan kawara wajen fitar da 'yan takara."
Ya ce babban dalilin da ke sanya 'ya'yan jam'iyyar mai mulki wannan dambarwa shi ne "shirye-shirye da kulle-kulle kan yadda zaben 2023 zai kasance."
"Wasu gagga-gaggan jam'iyyar ta APC ne ke ta kokarin ganin sun karbe iko ko kuma akalar jam'iyyar domin ganin cewa su ne za su yi nasara a lokacin zaben 2023."
Dangane kuma da makomar jam'iyyar, Dr Kari ya ce " babu wanda zai iya cewa ga makomarta amma dai za ta iya darewa tun da da ma APC, jam'iyyar hadaka ce kuma har yanzu ba ta dunkule wuri guda ba."












