Coronavirus: Ku yi Sallar Idi a gidajenku – Sarkin Musulmi

Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar Jama'atu Nasril Islam (JNI) ƙarƙashin jagorancin Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji (Dr.) Muhammad Sa'ad Abubakar III, ta ce bai kamata a yi taron Sallar Idi ba saɓanin yadda wasu jihohi ke bayar da damar yi.
Kwamitin fatawa na ƙungiyar ƙarƙashin jagorancin Sheikh Sheriff Ibrahim Saleh Alhusainy ya tatattauna tare da fito da matsayarsu game da sallar yayin annobar korona kamar haka:
- Bai kamata a yi jam'in Idi a cikin birane da wajensu ba
- Mutane su yi Sallar Idi a gida tare da iyalansu ko kuma mutum ya yi shi kaɗai idan babu kowa tare da shi
- a- Sallar Idi raka'a biyu ce tare da kabbara bakwai (7) a raka'ar farko haɗi da kabbarar farko, sannan a karanta fatiha da kuma wata sura - an fi son a karanta Suratul A'ala wato Sabbi
- b- A raka'a ta biyu kuma za a yi kabbara biyar (5) sannan a karanta fatiha da kuma wata sura - an fi so a karanta Suratul Gashiyah wato Halataka
- Idan za a yi Sallar Idi a gida ba sai an yi huɗuba ba
- Dukkanin abin da aka faɗa a sama daga mazahabar Imam Malik aka ciro su a littafin Mukhtasar
- A jihohin da aka bayar da damar yin Sallar Idi, ya kamata a yi amfani da masallatan cikin unguwa idan ya zama dole. A bi sharuɗɗan da masana harkar lafiya suka bayar na saka takunkumi da wanke hannu da yin nesa-nesa da juna
- Malamai su ji tsoron Allah su kiyaye harshe da kuma ayyukansu domin kare mutuncin addini da kuma Musulmai
Ranar Asabar ko Lahadi ake sa ran yin Idin Ƙaramar Salla, kuma tuni jihohi irinsu Kano da Borno da Jigawa da Adamawa da Gombe suka bayar da damar buɗe masallatan Idi domin gudanar da sallar da ake yi saboda kawo ƙarshen azumin watan Ramadana.
Sai dai gwamnatin tarayyar Najeriya na ƙorafi kan sassauta dokokin kulle da gwamnonin ke sassautawa a jihohinsu, inda ta ce "muna tufka jihohi na warwarewa" a yaƙin da ake yi da annobar korona a ƙasar.







