Bello Matawalle: Yadda gwamnonin Arewa Maso Yamma za su yi galaba kan 'yan fashin daji

Gwamnan Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya, Bello Matawalle ya bai wa al'ummar jihar tabbacin cewa ɗaukacin manoman Zamfara sai sun noma gonakinsu a bana.

Ya ce suna nan suna tsara yadda za a yi. "Insha Allahu, ina tabbatar ma Zamfarawa in Allah Ya yarda wannan damuna kowa zai yi noma".

Yayin wata zantawa kai tsaye da BBC a shafukan sada zumunta, gwamnan ya ce yana ci gaba da tattaunawa da jami'an tsaro ciki har da kwamishinan 'yan sanda "domin wasu daga cikin tubabbun 'yan bindiga sun same shi sun nuna baƙin cikinsu da waɗannan hare-hare da ake kai wa."

Mutanen yankunan karkara da yawa ne suka kwashe tsawon lokaci ba tare da sun iya noma gonakinsu ba a yankin jihar Zamfara da ma sauran wasu jihohi masu makwabtaka da ita saboda hare-haren 'yan fashin daji.

Gwamna Mutawalle ya ce: "Tubabbun 'yan fashin dajin da gwamnatinsa ta cimma sulhu da su, sun tabbatar da cewa za su bi sauran takwarorinsu waɗanda ake zargi su ne har yan zu ke kai hare-hare don tsawatar musu a karon ƙarshe."

A cewarsa; "Yanzu haka ranar Talata na ba da damar a ba da eka 100,000 wadda ƙungiyar manoman auduga ta nema don bunƙasa noman auduga da rage yawan marasa aikin yi wanda Babban Bankin ƙasar zai tallafa."

Ya ce Allah Ya hore wa jiharsu ta Zamfara faɗin ƙasa da kuma ma albarkar ƙasar noma. "Don haka i(da)n Allah Ya yarda za ai noma kuma mutane za su amfana".

Tagomashin Bello Mutawalle ya fito fili ne bayan hawansa kan karagar mulki bara, da kuma ƙoƙarinsa wajen rage hare-haren 'yan fashin daji da jihar ke fama da su tsawon shekara tara.

Ko a farkon wannan mako, wata kungiya mai bincike kan tashe-tashen hankula a duniya, International Crisis Group, ta ce fiye da mutum 8,000 aka kashe a rikice-rikice da hare-haren da suka addabi yankin cikin shekara goma.

Kungiyar ta ce lamarin ya kuma raba fiye da mutum 200,000 da muhallansu cikin waɗannan shekaru.

A wani rahoto da ta fitar ranar Litinin, ƙungiyar ta ce kawo yanzu ƙoƙarin hukumomi ya gaza kawo ƙarshen ire-iren waɗannan tashe-tashen hankula, da suka fi shafar jihohin Zamfara da Sokoto da Katsina da Neja da kuma Kaduna.

Shi dai Bello Mutawalle ya ce matuƙar gwamnonin yankin ba su ɗauki gabarar magance rikice-rikicen da kansu ba, mai yiwuwa ne a ci gaba da samu wannan matsala ta taɓarɓarewar tsaro a yanki.

"Idan ma taro za a yi da irin waɗannan mutane da suka ce sun yarda da sulhu, to su ga gwamnonin mun taru gaba ɗaya. Kuma maganar da muka cimma a tabbatar an ɗauki matakan aiwatarwa nan take," in ji Gwamna Mutawalle.

Ya kuma ce babu wanda zai je daga wuri ya magancewa al'ummominsu matsalolin da suke ciki face su da kansu gwamnonin yanki.

A cewarsa: "Duk yadda muke tunanin mu sa wani ya yi wani abu, wallahi ba zai yi yadda ya kamata a yi ba. Ita ce gaskiyar magana!"

Gwamna Bello ya ce masu kai irin waɗannan hare-hare abin da suke kuka shi ne an mayar da su tamkar na-baya ga dangi a Najeriya. "Idan wasu shirye-shirye sun zo na gwamnatoci ba a sanya wa da su."

"Wani bin ma kasuwar da ya kamata su tai ci, su samu abinci ko su sayar da dabbobinsu, ba a bari. Idan an gan su sai a kashe su ko kuma a kama dabbobinsu, ka ga wannan zalunci ya shiga.

Kuma duk inda za a samu shugabanni suna zalunci ba yadda za a yi ƙasar nan ta zauna lafiya," cewar Bello Mutawalle.