Rashin Tsaro: Sojojin Nigeria sun kashe 'yan fashi 27 a Zamfara

Lokacin karatu: Minti 1

Hedikwatar rundunar sojojin Najeriya da ke Abuja, babban birnin ƙasar ta ce ta halaka 'yan fashi 27 a kan iyakar jihohin Zamfara da Katsina.

A samamen da rundunar tsaro ta musamman mai laƙabin Hadarin Daji ta kai wa 'yan fashin ranar Alhamis, an kashe su tare da lalata wasu daga cikin sansanoninsu bayan samun wasu bayanan sirri, kamar yadda rundunar ta bayyana a wata sanarwa a shafinta na Twitter.

Rundunar ta ƙara da cewa bayan samun rahotannin sirrin ne kuma ta bazama, inda jiragenta mai saukar ungulu da kuma mai kai hari ta sama suka isa matsuguninsu da ke haɗakar garuruwan Nahuta da kuma Doumborou.

A baya-bayan nan sojoji na bayyana irin nasarar da suke samu a kan masu ɗauke da makamai, sai dai babu wata kafa mai zaman kanta da ke tabbatar da nasarorin.

Gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Muhamnmadu ta ce tana bakin ƙoƙarinta amma ko a ranar 20 ga watan Afirlu an samu rahoton mutum 47 da 'yan bindiga suka kashe a Katsina.

Yankin jihohin Zamfara da Katsina da Sokoto suna fama da hare-haren 'yan fashi a baya-bayan nan kuma hakan ya haddasa rasa rayuka da dama tare da raba wasu da mahallansu.