Muna kukan rashin Shugaba Umar 'Yar Adua - Jonathan

Yau ne tsohon shugaban Najeriya, Umaru Musa 'Yar adua yake cika shekaru 10 cif-cif da rasuwa, inda ya kwashe kimanin watanni biyar yana jinya kafin daga bisani Allah ya karbi ransa.

Tsohon Shugaban Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan ya ce ba zai taba manta wa da wannan rana ba ta rashin mai gidansa kuma abokin aikinsa, marigayi Umaru 'Yar adua.

"Shekaru 10 kenan tun bayan da mutuwa ta dauke shugaba Umaru Musa 'Yar'adua. A rana irin wannan tunaninsa na bujuro mana sannan muna tuna irin halayyar kankan da kai na marigayin wanda yake da shi daban da mutane.

Y'ar adua ya kasance shugaban da ba a taba yi ba wanda ya koma ga ubangijinsa yana mai kishin kasarsa. Ba dare ba rana, tunaninsa shi ne jama'arsa."

Mista Jonathan wanda ya karasa shekaru biyu na mulkin 'Yar adua kafin a sake zabarsa a 2011, ya kara da cewa "Shugaba 'Yar adua ne ya dasa dan-ba na kishin kasa da kauna da faimtar juna a tsakanin 'yan Najeriya, al'amairn da ya zamo hanyar samar da sauyin da ake bukata a kasar.

Shugaba Umaru 'Yar adua ya yi fice ta hanyoyi da dama. Mutum ne mai sauraron jama'a, kawaici da kuma son gyara kasa, inda ya koma ga ubangiji ya kuma bar wannan gagarumin aikin a hannun wanda ya gaje shi.

Ba shakka shugaba Umar ya bar abubuawar alkairi ga kasa da suka hada da dimokradiyya da mutunta 'yancin dan adam da kuma dokokin kasa."

Daga karshe tsohon shugaba Jonathan ya sha alwashin ci gaba da "tuna wa da abokin aikinsa kuma mai gidansa sannan dan uwa mai kama da aboki."