Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus: Yadda na sha fama da cutar - Muhammad Atiku Abubakar
Latsa bidiyon da ke sama domin kallon hira da Mouhammad Atiku:
Muhammad Atiku, ɗan tsohon mataimakin shugaban ƙasar Najeriya Atiku Abubakar, ya bayyana wa BBC halin da ya shiga lokacin da ya kamu da cutar korona.
A makon jiya ne aka sallami Muhammad Atiku -- wanda ke cikin mutane na farko-farko da suka kamu da cutar a Abuja -- daga cibiyar killace masu fama da cutar bayan ya shafe kwana arba'in a killace, kuma hakan ne ya sa shi kasancewa cikin mutane da suka fi daɗewa suna jinyar cutar ta korona.
Ga cikakkiyar hirar su da Salihu Adamu Usman:
Tambaya: Daga karshe dai an ayyana ka a matsayin wanda ya warke daga cutar korona bayan shafe kwana arba'in kana killace, yaya kaji da hakan?
Amsa: Godiya ga Allah maɗaukakin sarki, kuma bayan haka godiya ga 'yan uwa da jama'a wadanda sukayi mana fatan alkhairi.
Gaskiya a wancan lokacin an shiga wani irin yanayi amma Alhamdulillah an fito da rai da lafiya.
Yanayin shi ne ba lallai na alamomin cutar ba amma kamar tunani da damuwa saboda rashin sanin abunda zai faru daga baya.
Don haka dole hankalin mutum zai ɗan tashi, amma Alhamdulillah duk wannan yanzu ya zama tarihi, kuma dama mun ɗauki wannan lokaci tamkar jarrabawa ce daga Allah kuma mun gode masa.
Tambaya: Shin ko ka fuskanci wata fargaba a lokacin da kake killace?
Amsa: E, hakika gaskiya na ɗan yi fargaba saboda kasan kana zaune a wuri ɗaya; sati ɗaya, sati biyu, sati uku, mutane tsofaffi da yara da mata da maza suna zuwa su shiga jinya sai su riga ka warkewa su tafi kai kuma kana nan baka san halin da kake ciki ba, babu kuma wanda ya isa ya gaya maka ga abunda yake damunka, ga ni kuma matashi kuma Alhamdulillahi bana fama da wata rashin lafiya da zata jawo mini illa kaga dole mutum ya shiga halin fargaba.
Ga shi ban ji alamar wata illa ba, ko alamar wata rashin lafiya.
Ko tari ma da zazzaɓi da ake cewa aka fi yi idan cutar ta kama mutum duk banji suba.
Tambaya: Zan iya tunawa ance an kai ka ɗakin kula da marasa lafiya na musamman wato ICU. Haka ne?
Amsa: Duk wannan ba gaskiya ba ne, yadda dai na shiga wurin haka na fita babu wata alamar rashin lafiya. Baza ka ɗauka akwai wani abunda ke damuna ba ma, yadda ka ganni yanzu haka nake inanan garau.
Tambaya: Ayayin da mutane da dama ke kwana 14 kacal su warke kai kuma sai da ka shafe kwana 40, waɗanne dalilai ne likitoci suka bayyana maka kan rashin warkewa da wuri?
Amsa: Likitoci basu bada cikakken bayani ba saboda wannan cutar sabuwa ce a duniya baa gama fahimtar ta ba, saboda haka sun kasa gane dalilin da yasa cutar ta daɗe har ta kai kusan makwanni 5 a jikina.
Tambaya: Ka faɗa mana abubuwa biyar da mutane basu sani ba game da cibiyoyin killace masu cutar korona.
Amsa: Na ɗaya, ba wai wuri ne da mutum zai tayar da hankalin shi ba saboda ba a gida kake ba.
Wani wuri ne dai da zaka kasance tare da wasu marasa lafiya kuma zaa samu ku ido, ana baku magani kuma ana kula da ku tare da tambayar ku yadda kuke ji.
Ba wani wuri ne da yake da tsari sosai ba, idan kana wurin dai sai ka kula sosai domin za'a rika cewa sai ka sanya takunkumin fuska, sannan ace kada ka rika zuwa kusa da mutane kamar yadda aka fara yi a cikin gari amma anfi sa'ido a can.
Bayan haka kuma babu wani bambanci da zaman gida saboda kana tare da wayarka da na'urar kwamfutar ka sannan kana Magana a waya duk lokacin da kake so.
Tambaya: An taba baka damar yin waya da iyalanka? Misali matar ka ko 'ya'yan ka ko kuma mahaifin ka a lokacin da kake killace?
Amsa: Sosai ma, babu wanda zai hana ka abunda kake so kayi game da waya ko jin kida duk lokacin da kakeso kayi zaka yi.
Bayan haka kuma zaka iya haduwa da mutane amma daga nesa za'a bada tazara, za'a iya yin mu'amala nan da can.
Ba wani wuri ba ne na tayarda hankali, bayan haka kuma gwamnati za ta kula da kai, ita za ta baka abinci da komai.
Tambaya: Yaya zaka bayyana yadda rayuwa take a cikin cibiyoyin killace masu cutar korona a takaice?
Amsa:Bazan ce kamar gidan yari bane amma kana zaune ne a wuri daya babu damar yin walwala sosai, amma zaka samu kula da wurin kwanciya da wutar lantarki, to kaga kenan wurin babu laifi. Gwamnati tayi kokari a wannan bangaren.
Tambaya: A lokacin da kake killace ka wallafa wani bidiyo inda kake nuna damuwa kan labaran kariya da ake yadawa a intanet, me yasa ka damu kan irin wadannan labaran?
Amsa: A lokacin ana ta wasu maganganu marasa kan gado, kuma duk wanda yake cikin wani hali hakan zai iya tada mishi hankali.
Saboda haka shi yasa na jawo hankalin mutane don su maida hankali, bai kamata kowace maganar da akaji ba a dauke ta tamkar gaskiya saboda akasari ba gaskiya ba ne.
Shi yasa na fito nayi Magana bawai don kaina kawai ba amma amadadin duk wadanda suka samu kansu cikin wani yanayi.
Abinda ya kamata mutane su sani shi ne wannan cutar jarrabawa ce daga Allah, kuma dole mu roke shi ya yaye mana ita a duniya baki daya mu nemi kariyar sa.
Tambaya: Anyi ta rade-raden cewa kaje wuraren shakatawa da masallatai sannan ka gana da mutane daban-daban sannan kuma sai da aka killace ka bisa tilas, menene gaskiyar al'amarin?
Amsa: Duk maganganu da akayi babu gaskiya ko daya a cikin su, saboda ni da kaina na kira jami'an kiwon lafiya da yake na dawo daga kasar waje nace musu na dawo daga cikin kasashe da ake fama da cutar korona don haka su zo su gwada ni saboda in san matsayi na.
Bayan sun zo sun gwada ni kuma kaddara ta nuna cewa inada cutar sai suka zo washe gari suka daukeni suka kaini wajen killace mutane.
Tambaya: Shin ko kana ga anyita yada wadannan labaran kanzon kurege ne akanka saboda kasancewar ka dan wanda ya taba takarar neman shugabancin Najeriya wato Alhaji Atiku Abubakar?
Amsa: E, yana iya yiwuwa haka ne saboda dama muddin ka fito daga babban gida ko kanada wanda ya taba rike wani mukami dama akanyi magana akanka amma bawai wani abu bane.
Ni da akayi akai na bai dame ni sosai ba saboda tun ba yau ba mun saba, amma kaga wasu ba haka zasu dauki abun ba da sauki yadda kai ka dauka shi yasa na fito nayi magana.
Tambaya:Wane sako kake da shi ga likitoci wadanda suka sadaukar da rayuwar su wajen jinyar masu dauke da cutar korona da kuma masu fama da ita?
Amsa: Ina musu addu'ar Allah ya saka musu da alkhairi, ya kare su, kuma muna rokon gwamnati ta kula da su, ta kula da iyalan su da kuma lafiyar su.
Ga wadanda suke fama da cutar korona, su san cewa ba wata cuta ceda za ta jawo musu illa sosai ba, su tsaya su rike addu'a, su kula da kansu sannan su bi dokokin da shawarwari da likitoci ke bayarwa sannan kar su tayar da hankali ko kadan domin idan suka tayar da hankalin su to za su yi ta rikicewa.
Tambaya: Menene sakon ka ga 'yan Najeriya da aka bai wa damar fita da kuma komawa aiki daga ranar Litinin hudu ga watan Mayu?
Amsa:Sakon da zan isar musu shi ne su bi dokokin gwamnati game da bada tazara da kuma sanya takunkumin fuska, su kare kansu ko ba don su kadai ba amma don 'yan uwansu da kuma iyalansu.
Tambaya: Ganin cewa ka samu lafiya menene babban burinka a yanzu?
Amsa: Wallahi babu abunda na saka a gaba illa in kara kusantar da kaina ga ubangiji, inci gaba da mu'amala mai kyau da jama'a; da kuma mutunta mutane da kuma zaman lafiya da su.
Bayan haka kuma ina tunanin komawa makaranta in karo ilimi.
Tambaya: Wannan buri ne da ka fara shi bayan warkewa daga cutar korona ko tun dama yana nan?
Amsa: Wannan buri ne na ko yaushe. Amma wani lokaci sai ka shiga cikin wani hali zaka samu kayi nazari mai zurfi, da zarar kayi haka kuma sai kaji niyyar da kake da ita ta karfafa.
Tambaya: Wanne babban darasi ka koya kan wannan abunda ya faru da kai?
Amsa: Babban darasi da na koya shi ne addu'a itace maganin komai, a koda yaushe mu dogara ga Allah mu rokeshi zai amsa ma na.
Kuma bayan haka bamu san yaushe karshen mu zai zo ba, ba mu san yaushe lokacin mu zai zo ba saboda zai iya zuwa a ko da yaushe don haka mu dauki kowa da muhimmanci mu mutunta mutane.
Wannan shi ne babban darasi da na koya sakamakon hali da na shiga.