Sarakuna masu daraja ta Ɗaya da suka mutu a Najeriya

Arewacin Najeriya ta yi rashin sarakuna masu daraja da Ɗaya da kuma wasu masu rike da sarautun gargajiya a jihohin Borno da Kano da kuma Zamfara a baya bayan nan.

Shehun Bama Kyari Ibn Umar Elkanemi

Ranar Litinin 27 ga watan Afrilu ne aka sanar da rasuwar Shehun Bama, Kyari Ibn Umar Elkanemi a Maiduguri, babban birnin jihar Borno. Sanarwar da Kwamishinan harkokin ciki gida da yada labarai na jihar, Babakura Abba Jato, ya fitar ya ce basaraken ya mutu ne yana da fiye da shekara 60 a duniya.

Jato ya ce Shehun na Bama ya daɗe yana fama da rashin lafiya irin wacce masu shekaru irin nasa suke fama da ita.

Sarkin Rano Alhaji Tafida Abubakar Ila

A ranar Asabar 2 ga watan Mayu ne Allah Ya yi wa Sarkin Rano Alhaji Tafida Abubakar Ila rasuwa a asibitin Nasarawa da ke birnin Kano a arewacin Najeriya.

Tuni aka yi jana'izarsa a garin Rano a yammacin ranar.

Alhaji Tafida Abubakar Il ya rasu ne bayan gajeriyar jinya, yana da shekara 74, kamar yadda Kabiru Alhassan Rurum, dan majalisar tarayya mai wakiltar Rano da Bunkure kuma Turakin Rano ne ya tabbatar wa BBC labarin rasuwar.

Mai magana da yawun Masarautar Rano Wali Ado ya ce Sarkin ya yi jinyar kwana biyar ne, inda aka kai shi asibiti a ranar Juma'a.

Yana daga cikin sarakuna hudu masu daraja ta daya na sababbin masarautun jihar da Gwamna Abdullahi Ganduje ya kirkira a bara.

Wali Ado ya ce dama Sarkin yana da cutar hawan jini da ciwon suga da ke taso masa lokaci-lokaci.

Autan Bawo -- kamar yadda aka fi sanin sa -- ya rasu ya bar ata biyu da 'ya'ya 17, 12 maza, biyar mata.

Sarkin Ƙauran Namoda Muhammad Ahmad Asha

Allah Ya yi wa mai martaba Sarkin Kiyawan Ƙauran Namoda a jihar Zamfara Alh. Muhammad Ahmad Asha rasuwa bayan shekara 16 a gadon sarauta.

Sarkin ya rasu ne da safiyar Lahadi, 3 ga watan Mayu bayan gajeruwar rashin lafiya, kamar yadda wani na kusa da fadar Ƙaura Namoda ya tabbatar wa BBC.

Amma Sarkin ya dade yana fama da hawan jini da kuma ciwon suga.

Shi ne Sarki na biyu a tarihin sarautar Sarki mai sanda ta Emir mai daraja ta ɗaya a Ƙauran Namoda bayan mahaifinsa, amma shi ne Sarki na 16 a masarautar Kiyawan Ƙauran Namoda.

Sarkin ya rasu yana da shekara 71 a duniya, kuma ya bar mata uku da ƴaƴa.

Jarman Kano Farfesa Isa Hashim ya kwanta-dama

Shi ma Jarman Kano, Farfesa Isa Hasim, ya rasu.

Ya rasu ne a ranar Lahadi yana da shekara 86, kamar yadda wani surukinsa ya tabbatar wa BBC.

Babu dai wani cikakken bayani kan dalilin rasuwarsa.

Marigayin ya soma aiki ne a Kano Native Authority a 1948 kuma ya kai matakin babban sakatare kafin ya yi ritaya a 1979.

Bayan ritaya ne, Farfesa Isa Hashim ya koma bangaren koyarwa a Jami'ar Bayero da ke Kano, inda kwashe shekaru da dama yana koyarwa a fannin siyasa.