Coronavirus: Ganduje ya sassauta dokar hana fita a Kano

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano ya sassauta dokar hana fita da Shugaba Muhammadu Buhari ya saka ta tsawon kwana 14.

Yanzu mazauna birnin Kano za su iya fita a ranakun Litinin da Alhamis daga karfe 10:00 na safe zuwa 4:00 na yamma, kamar yadda wata sanarwa ta bayyana.

Sai dai gwamnan ya ce manyan kantunan sayayya ne kadai za su bude, yayin da kasuwanni za su ci gaba da kasancewa a rufe.

Sannan ya ce za a sanar da sunayen kantunan da za su bude din a gidajen rediyon da ke jihar.

Har wa yau sanarwar ta ce Gwamna Ganduje ya zabi kasuwannin 'Yan Kaba da Na'ibawa 'Yan Lemo su yi harkoki a ranakun Litinin da Alhamis daga karfe 10:00 zuwa 4:00.

A jawabinsa na ranar Talata ga 'yan Najeriya, Shugaba Buhari ya saka dokar hana fita ta tsawon mako biyu a Jihar Kano sakamakon karin yawan mutanen da ke kamuwa da cutar korona.

Sai dai Buhari ya sassauta dokar a Abuja da kuma jihohin Legas da Ogun daga ranar Litinin mai zuwa, inda mazauna garururwan za su yi zirga-zirga daga karfe 6:00 na safe zuwa 8:00 na dare.