Majalisar Najeriya ta amince wa Buhari cin bashin Naira biliyan 850

Majalisar dattawan Najeriya ta amince wa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya karbo rancen kudi naira biliyan 850.

Majalisar ta amince da bukatar ne a zaman da ta yi ranar Talata bayan ta dawo daga hutun cutar korona.

Shugaba Buhari ya bukaci majalisar ta amince da bukatarsa ta samun rancen daga kasuwar kudi ta cikin gida domin bai wa gwamnatinsa damar aiwatar da kasafin kudin 2020.

Najeriya dai ta samu wagegen gibi daga kudaden da take samu bayan farashin danyen mai ya fadi da kusan kashi 45 cikin 100.

Faduwar farashin danyen mai ya sa gwamnatin Najeriya ba za ta iya aiwatar da kasafin kudinta ba na shekarar 2020 ba tare da ta nemi taimako ba.

Gwamnatin ta tsara kasafin ne kan dala 57 duk ganga kafin sake sauya hasashen zuwa dala 30 duk ganga.

Yanzu kuma farashin danyen mai ya fadi zuwa dala 20 duk ganga a ranar Talata.

Farashin man na ta faduwa ne sakamakon annobar cutar korona da take yi wa fannonin rayuwa daban-daban da suka hada da na tattalin arzikin rugu-rugu.