Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Fitattun mutane 11 da suka mutu a Kano cikin kwana hudu
A cikin kwana biyu jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya ta yi rashin manyan fitattun mutane da suka hada da malaman jami'a da kwaleji da malaman Islama da ma'aikata.
Mutuwar tasu ta zo ne a daidai lokacin da ake ta kokawa kan yawan mace-macen da ake samu a jihar, wadanda suka tayar da hankalin al'umma.
Duk da cewa ana samun mace-macen a daidai lokacin annobar cutar korona da ta gallabi duniya, babu wani tabbaci kan ko ita ce ta ke kashe mutane da yawa haka.
A ranakun Asabar da Lahadi ne aka samu mace-mace da dama da suka hada da na wadannan malamai.
An yi ta alhini da jimamin mutuwar wadannan bayin Allah a shafukan sada zumunta.
Ga dai bayanai kan wadannan manyan masana ilimi.
Farfesa Ibrahim Ayagi
Farfesa Ibrahim Ayagi ya rasu a ranar Asabar 25 ga watan Afrilun 2020. Iyalansa sun sanar da cewa ya rasu bayan wata rashin lafiya da ba a bayyana ba.
Ayagi haifaffen jihar Kano ne kuma farfesa ne a kan Tsimi da Tanadi. An haife shi a shekarar 1940.
Ya yi karatun firamare a Dandago Primary School da kuma Gwarzo Primary School daga 1950 zuwa 56.
Ya je Kwalejin Horas da Malamai ta Wudil daga 1958 zuwa 1960; sai Katsina Teachers College, 1962 zuwa 1963; sai Jami'ar Ahmadu Bello (ABU) Zaria, daga 1963 zuwa 1970 inda daga nan ya wuce Jami'ar Pittsburgh da ke Pennsylvania a Amurka daga 1970 zuwa 1974.
Shi ne wanda ya kafa fitacciyar Makarantar Hassan Ibrahim Gwarzo da ke Kano. Ya yi aiki a wurare da dama ciki har da BBC Hausa.
Farfesa Aliyu Umar Dikko (1953-2020)
Dan asalin jihar Kano ne. An haife shi a shekarar 1953. Ya mutu ranar Asabar yana da shekara 67.
Shi ne Bahaushe na farko da ya zama farfesa na farko a Bangaren Sassan Jiki. Yana koyarwa ne a Jami'ar Bayero.
Shi ne shugaban Tsangayar Koyon Aikin Likita a Jami'ar Maitama Sule da ke Kano kafin mutuwarsa.
Ya mutu ya bar mata daya da 'ya'ya bakwai da jikoki bakwai.
Farfesa Balarabe Maikaba
Farfesa Balarabe Maikaba ya rasu a ranar Lahadi 26 ga watan Afrilu bayan fama da zazzabi na 'yan kwanaki kamar yadda rahotanni suka ce. Amma dama yana dauke da ciwon suga.
Farfesa Maikaba dan asalin karamar Hukumar Fagge ne da ke jihar Kano. Ya yi karatunsa na firmare da sakandare a Kano sannan ya je Jami'ar Bayero inda ya yi digirinsa na farko a bangaren aikin jarida.
Ya yi digiri na biyu a Jami'ar Ibadan sannan digirin-digirgir a Jami'ar Bayero. Ya shafe shekaru da dama yana koyarwa a sashen Koyon Aikin Jarida a Jami'ar Bayero.
Ya mutu ya bar mata hudu da 'ya'ya 16.
Dr. Sabo Kurawa
Dr Sabo Kurawa ya rasu a ranar Asabar 26 ga watan Afrilun 2020. Iyalansa sun ce dama ya dade ba shi da lafiya.
An haife shi a watan Yulin 1949. Ya yi karatun firamare a Kurmawa Primary, ya yi makarantar sakandare a Teachers College da ke Wudil, ya yi NCE a Zaria, sai digirinsa na farko a Jami'ar Ahmadu Bello inda ya karanta sanin halayyar dan adam, Sociology.
Ya yi karatun digiri na biyu da na uku a Jami'ar Evanston da ke jihar Illinois ta Amurka a bangaren Political Sociology. Kuma shi ya fara gabatar da karatun Criminology da Social Policy, kamar yadda matarsa ta shaida wa BBC.
Ya taba rike mukamin mataimakin shugaban Jami'ar Bayero har sau biyu da DVC Admin da DVC Academy.
Ya fara aiki a shekarar 1978 a matsayin malami a BUK.
Ya mutu ya bar mace daya, Farfesa Dijeh Kurawa malama a Sashen Ilimin Akanta a BUK da kuma yara shida.
Daga cikin yaransa akwai Nafisa Kurawa babbar ma'aikaciya a hukumar CAC Abuja da Najib Kurawa, malami a Jam'iar Tarayya Ta Dutse, akwai kuma dan sanda cikin yaran nasa.
Dr Uba Adamu (1935-2020)
Dokta Muhammadu Uba Adamu malamin jami'a ne a bangaren Tarihin Siyasa a makarantar Kano State Polytechnic kafin ya yi ritaya a shekarar 1995.
Ya rasu ranar Litinin 27 ga watan Afrilun 2020. Amma sun ce bai yi tafiya zuwa wata kasa ba a baya-bayan nan.
Dokta Muhammad shi ne mahaifin shugaban Jami'ar Koyo Daga Gida Ta Najeriya Farfesa Abdallah Uba Adamu.
Dr Ghali Kabeer Umar
A ranar Litinin ne shugaban Jam'iar Fasaha Ta Wudil a jihar Kano Farfesa Shehu Alhaji Musa ya sanar da rasuwar Dr Ghali Kabir Umar na Sashen Ilimin Zane-Zanen gine-gine na makarantar.
Duk da cewa babu wani cikakken bayani kan mamacin, amma ya taba rike shugaban Sashen limin Zane-Zanen gine-gine na Jam'iar Fasaha Ta Wudil.
Ba a dai fadi abin da ya yi sanadin mutuwar tasa ba.
Ustaz Dahiru Rabi'u (1948-2020)
Shi ne tsohon Alkalin alkalan jihar Kano. Ustazu Dahiru Rabi'u malamin addinin Islama ne. Duk da cewa ba ya fama da wata cuta da aka san shi da ita, amma iyalansa sun ce ya rasu ne sakamakon zazzafan zazzabi.
Abdullahi Lawal
Kafin mutuwarsa marigayi Abdullahi ne shugaban yanki na bankin First Bank a Kano. Ana zargin cewa cutar korona ce ta kashe shi.
Majiyoyi sun ce a ranar Asabar aka garzaya da marigayin wanda ke da shekara 50 da 'yan kai zuwa wani asibiti mai zaman kansa sakamakon zazzafan zazzabi, da tari da kuma shakuwa. Amma sai ya rasu ranar Lahadi.
Wani sakon murya ya yadu a shafukan sada zumunta da muryar wata mata da take ikirarin cewa ita surukarsa ce, tana tuhumar hukumar dakile yaduwar cututtuka ta Najeriya reshen Kano, da cewa sakacinsu ne ya kashe mata mijin 'yarta.
Musa Ahmad Tijjani
Marigayi Musa Ahmad Tijjani tsohon dan jarida ne kuma tsohon editan Jaridar Leadership Sunday ne da kuma jaridar Triumph da ake wallafawa a Kano.
Marigayin dan jaridar ya yi korafin zazzafan zazzabin da ya sa aka kwantar da shi a asibiti na tsawon mako daya, kafin daga bisani ya rasu a ranar Asabar 25 ga watan Afrilun 2020.
Sheikh Tijjani Tukur Yola
Sheikh Tijjani Tukur Yola fitaccen malamin Addinin Musulunci ne na Darikar Tijjaniya. Sheikh Tijjani alkali ne, kuma babban limamin Masallacin Murtala a Kano.
Ya rasu a ranar Litinin 27 ga watan Afrilun 2020 yana da shekara 86.
Hajiya Halima Shitu (1963-2020)
Malama Halima Shitu mata ce ga fitaccen Malamin Islama Sheikh Abdulwahab Abdullah.
Tana daya daga cikin tsirarun mata malamai a Kano, kuma ita ce macen da ta fara tafsiri cikin malamai mata.
An haife ta a unguwar Yakasai a shekarar 1963 kuma ta yi karatunta na firamare ne a Shahuci da sakandare a Dala. Bayan ta auri Sheikh Abdulwahab ne sai suka tafi Madina inda yake karatu a lokacin.
A can ta yi karatun difloma a fannin Larabci sannan ta zarce da digiri a Kur'ani da Hadisi.
Yayarta Hajiya Halima Sani ta tabbatar wa BBC cewa ta rasu ne sakamakon zazzafan zazzabi na kwana hudu.
Ta mutu ranar Litinin da dare ta bar yara shida, mata biyu, maza hudu.