'Yan bindiga sun kashe mutum 47 a Katsina

Aminu Bello Masari

Asalin hoton, KSG

Wasu 'yan bindiga haye a kan babura sun kai hari kananan hukumomin Safana da Dutsinma da Danmusa na jihar Katsina, inda suka yi ta harbin kan-mai-uwa-da-wabi tare da cinna wa gidajen jama'a wuta.

Maharan dai sun kashe akalla mutum 47, a yayin harin da suka kai kauyuka kusan 10 da ke kananan hukumomin guda uku, a cewar rundunar 'yan sandan jihar.

Rundunar 'yan sandan jihar ta Katsina ta ce da misalin karfe dayan daren ranar Asabar ne dai maharan suka shiga kauyukan.

Sai dai wani mazaunin daya daga cikin garuruwan da al'amarin ya faru ya shaida wa BBC cewa sun kirga gawa 73 ban da wadanda aka nema aka rasa.

Ya kuma kara da cewa "'yan bindigar da ke kan babura fiye da 150 sun ci karensu babu babbaka ba tare da jami'an tsaro sun kawo mana dauki ba.

Suna bin mutane a kan babura suna harbi babu kakkautawa."

Tuni dai Shugaba Buhari ya yi Alla-wadai da harin inda ya ce 'yan bindigar na amfani da yanayin hana zirga-zirga da aka sanya sakamakon cutar korona.

Shugaban ya kuma shawarci 'yan Najeriya da ka da su yanke kauna dangane da kudirin gwamnati na ganin ta kawar da bata garin.