Coronavirus: Hanyoyi 5 da coronavirus ta shafi samar da abinci a duniya

Yayin da aka jefa al'ummar duniya cikin kulle, labarai da suka shafi karancin kayayyaki a kasuwanni da kantina ne suka mamaye kafofin sadarwa na Intanet.

Kamar yadda aka rufe kasuwancin gidajen cin abinci da wasu wuraren shakatawa, masu samar da abinci sun yi gargadin cewa suna da kayayyaki da yawa wadanda kuma za su iya lalacewa.

Wadannan wasu hanyoyi ne da annobar coronavirus ta yi tasiri ga samar da abinci a fadin duniya.

1. Raguwar samar da madara

Yayin da shagunan sayar da gahawa suka kasance a rufe a kasashe da dama, yawan madarar da ake samarwa na karuwa, wanda wata alama ce da ke nuna tasirin annobar coronavirus.

Manoman madara a Amurka, kungiyar manoman madara mafi girma, sun yi kiyasin cewa a duk rana kusan litar madara miliyan 14 manoma ke zubarwa saboda katsewar hanyoyin rarraba madarar ga 'yan kasuwa.

Wannan ba Amurka kawai ya shafa ba, manoma a Birtaniya sun nemi agajin gwamnati kan matsalolin da suka shiga. Peter Alvis shugaban kungiyar manoma ta Birtaniya ya ce kusan duk mako daya litar madara miliyan 5 ke cikin hatsari.

2. Lalacewar amfanin gona

Rufewa ya shafi dukkan fanoni na noma. Wasu manoman sun koma hulda kai-tsaye da kananan masu saya, amma sun sauya daga bukatun kasuwa na yau da kullum yayin da kuma kayayyakin da ke ajiye suka kasance babbar matsala a dukkanin bangarorin.

Jaridar New York Times, da ta tattauna da wasu manoman a Amurka, sun bayar da misali da yadda abubuwa suka sauka a kiwon kaji inda duk kaza daya ke kyankasa kwai 750,00 duk mako daya. An kuma yi magana da manoman albasa da suka ce suna fuskantar kalubale na samun wurin ajiye amfanin gonarsu.

A Indiya, masu noman ganyen shayi sun gargadin cewa matakan hana fita ya sa suna zaubar da amfanin gonarsu na ganyen shayin Darjeeling.

3. Karancin ma'aikata

Duk da samun yawaitar kayayyakin da ake samarwa da kuma kalubale na sauyawar kasuwancin zuwa ga kananan masu saya, manoma a a wurare da dama suna kuma fuskantar matsaloli na karancin ma'aikata.

Matakan killacewa da kuma bayar da tazara an bayar da rahotannin cewa suna raguwa a wurare, da kuma hana fita sun kasance matsala ga kwadago a masana'antar.

Makon da ya gabata Jamus ta daga kafa inda ta amince daruruwan 'yan kasashen Romania da Poland su shigo kasar domin su taimaka wa bangaren noma, musamman da aka shiga lokacin girbi.

Akwai kuma wani kamfen da aka kaddamar a Birtaniya na "ci da kasa" inda ake kira ga ma'aikata su taimaka domin datse duk wani gibi don kaucewa harasar abinci.

4. Sauya tsarin yadda muke sayayya

Annobar ta haifar da sauyi kan abubuwan da suka dace mu saya. Misali a Birtaniya an samu karuwar bukatar garin fulawa a makwannin baya inda mutane suke saya su ajiye domin yin abubuwan abinci da ake sarrafawa da fulawa.

Wasu alkalumma da kafar BFMTV ta bayyana, ya nuna cewa Faransawa sun koma sayen abincin da aka sauya wa halitta tun lokacin da coronavirus ta yi kamari a kasar.

Wannan saboda sun saba sayayya a kananan kantina - masana sun ce - mutane suna sun cin abinci mai kara lafiya lokacin annobar.

Wannan na zuwa yayin da ministan noma na Faransa ya yi kira ga jami'an kananan hukumomi su karfafa bude kasuwannin sayar da kayan abinci a sassan kasar.

A baya an bukaci a rufe su saboda tsaro, amma an fara budewa yayin da mutane suka saba da bayar da tazara a tsakaninsu.

5. Kaya a ajiye ba a amfani

Misali idan aka kwatanta da wuraren shan barasa da aka rufe a Birtaniya. Yawanci za a zubar saboda sun lalace.

Wasu kwalaben giya suna iya daukar makwanni kafin su lalace - wanda ke nuna zuwa lokacin da aka dage dokar hana fita dubbai ba za a iya sha ba.

Wasu a masana'antun sun yi gargadin cewa hakan na nufin za a yi hasara sosai.

...Amma ba mummunan labari ba ne ga wasu

Wasu bangarorin samar da abinci suna cin moriyar sauyin da aka shiga.

Kasuwancin lemu a Amurka, wanda ya fuskanci koma baya, an bayyana cewa ya karu da kashi 38% daga alkalumman shekarar da ya gabata.

Farashin lemu ya tashi a makwannin da suka gabata. "Barkewar cutar Covid-19 ya shafi samarwa da kuma bukatar lemu," kamar yadda Stephen Innes, na kamfanin AxiCorp ya ce a watan jiya.

"Abubuwan da ke inganta garkuwar jiki ana nemansa duk da cewa jirage ba su aiki da za su dinga jigilarsa zuwa kasuwanni."

Yawaitar bukatarsa babban labari ne ga manoman lemu, musamman a Florida da Brazil.