Wurin tsafi zai koma masallaci a Zamfara – Matawalle

Lokacin karatu: Minti 2

Gwamnatin jihar Zamfara ta ce za ta gina masallaci a gidan da ta rushe wanda aka yi zargin ana tsafi a garin Gusau.

A ranar Talata ne rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ta ce ta tarwatsa wani gidan da ta zarga na matsafa ne a garin Gusau inda ta samu wasu takardu dauke da sunayen manyan 'yan siyasa a jihar.

Bayan gano gidan ne kuma daga baya gwamnatin jihar ta bayar da umurni rusa shi.

A wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter wanda ba ya da alamar tantancewa, gwamnan jihar Bello Matawalle ya ce ya bayar da umurnin gina sabon masallaci a filin gidan 'tsafin' da aka rusa.

Sakon wanda mai taimakawa gwamnan Zamfara kan kafofin sadarwa na zamani Ibrahim Bello ya tabbatar cewa gwamna Matawalle ne da kansa ya rubuta a Twitter ya ce "Na bayar da umurnin gina sabon masallaci domin amfanar al'ummarmu ta musulmi."

Kwamishinan 'yan sandan jihar Usman Nagogo, ya ce jami'ansa sun kai samame ne gidan matsafan da ke Unguwar Dallatu bayan samun rahoto daga mutanen anguwar a ranar Litinin.

Ya ce sun samu abubuwa da dama da suka hada da: "Kwaryar jini da kwarya an sossoke allurai da wata tukunya dauke da gari da kuma takardun da aka rubuta sunayen shahararrun mutane a Zamfara."

A ranar Asabar rundunar 'yan sandan jihar ta ce, gwajin jinin da aka gudanar ya gano cewa jinin mutum ne ba na dabba ba, kamar yadda kakakinta ya tabbatarwa BBC.

Ya kuma ce ana ci gaba da gudanar da bincike game da al'amarin, musamman sunayen manyan 'yan siyasa da aka gani a rubuce a takardun da aka samu a gidan.

Har yanzu 'yan sandan ba su ce sun kama mutum daya ba da suke zargi bayan kwamishinan 'yan sandan jihar ya ce mutum biyu da aka iske a gidan dukkaninsu sun tsere.