Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Najeriya za ta rasa 45% na kudin shiga saboda faduwar farashin mai
Ministar Kudi ta Najeriya Zainab Ahmed Shamsuna ta ce Najeriya za ta rasa kusan kashi 45 cikin 100 na kudin shigarta da ta tsara za ta samu sakamakon faduwar farashin man fetur a kasuwar duniya.
Farashin danyen man fetur ya yi faduwar bakar tasa ne saboda kamun kazar kuku da annobar coronavirus ta yi wa manyan kasashen da suka fi sayen man irinsu China da kuma rashin cimma matsaya tsakanin Saudiyya da Rasha kan yawan man da za su rika fitarwa a kullum.
Ministar kudin tana wannan batu ne a ranar Laraba, inda ta ce hakan ya tilasta wa Najeriya ragewa da kuma kwaskwarima ga ayyukan da gwamnatin Buhari ta tsara za ta yi.
"Raguwar farashin man fetur daga dala 57 a kan kowacce ganga zuwa dala 30 da muka saka a kasafin kudi yana nufin cewa za mu yi asarar kusan kashi 45 cikin 100 na kudin shigarmu," in ji ministar.
"Saboda haka wajibi ne mu yi kwaskwarima ga wasu ayyuka da kuma kasafin kudi domin ya dace da abin da ke kasa."
Ministar ta kuma ce shugaban kasa ya bayar da umarnin a yi shirin ko-ta-kwana kan yadda za a yi ayyuka da farashin man na yanzu kan dala 30 a kowacce ganga daya.
"Wannan shirin gaggawa da za mu yi ya tilasta mu rage wasu ayyukan raya kasa duk da cewa muna ci gaba da duba hanyoyin habaka kudaden shigar da farashin man bai shafe su ba.
"Saboda haka za mu tabbatar cewa an ci gaba da hako ganga miliyan 1.8 da muka yi hasashe a kasafin kudi.
"Sannan kuma mun rage yawan kudin shigar da hukumar kwastam za ta samu daga tiriliyan 1.5 saboda mun fuskanci cewa kasuwanci zai ragu kuma idan kasuwanci ya ragu kudin shiga ma zai ragu."